logo

HAUSA

Mutane 108 sun mutum 92 sun jikkata a fashewar tankar mai a Saliyo

2021-11-07 16:01:39 CRI

Mutane 108 sun mutum 92 sun jikkata a fashewar tankar mai a Saliyo_fororder_A01-108 killed-Saliyo

A kalla mutane 108 ne suka mutu, kana wasu mutanen 92 sun samu raunuka sakamakon fashewar tankar mai da yammacin ranar Juma’a a kasar Saliyo, kamar yadda hukumar yaki da bala’u ta kasar NDMA ta tabbatar.

A sanarwar da hukumar ta NDMA ta fitar ta ce, wata tankar dakon mai makere da man fetur ne ta yi karo da wata babbar mota dake dauke da duwatsun kankare a wani babban titin mota yayin da tankar man ke kokarin shiga wani gidan mai don sauke man.

Wasu hotunan bidiyo da kuma shaidun gani da ido sun bayyana cewa, bayan faruwar hadarin, dukkan direbobin biyu sun fito daga motocin nasu inda suka gargadi al’umma mazauna yankin da su gaggauta barin wajen yayin da ake kokarin toshe kofar da man ke kwarara sakamakon taho mu gaman da motocin suka yi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A cewar sanarwar, jim kadan da faruwar lamarin, wasu mazauna yankin sun garzawa wajen da lamarin ya faru inda suka dinga kwasar man suna boyewa a wasu wurare dake kusa da wajen da hadarin ya faru. Sai dai yayin da suke tsaka da kwasar man, sai aka samu wata mummunar fashewa inda nan take wuta ta kama.

Shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya bayyana sakon ta’aziyyar hadarin fashewar tankar man, inda ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta yi bakin kokarinta wajen tallafawa iyalan mutanen da hadarin ya shafa.

Bugu da kari, shugaban kasar ya soke ziyarar da ya shirya yi don halartar taron shugabannin kasashen ECOWAS, wanda aka shirya gudanarwa a kasar Ghana a yau Lahadi. (Ahmad)