logo

HAUSA

Ina dalilin da ya sa kasa da kasa suka zabi kasar Sin don bullo da sabbin kayayyakin da suka samar?

2021-11-06 20:43:54 CRI

Ina dalilin da ya sa kasa da kasa suka zabi kasar Sin don bullo da sabbin kayayyakin da suka samar?_fororder_A

Daga ranar 6 zuwa 8 ga wata, a wajen bikin CIIE wato bikin baje-kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin da a yanzu haka yake gudana a birnin Shanghai, za’a fitar da wasu sabbin kayayyaki, da fasahohi gami da hidimomi, al’amarin da ya kasance karo na farko a duk duniya, ko a duk nahiyar Asiya ko kuma a nan kasar Sin. Hakan ba baiwa mutane damar kallon sabbin kayayyaki da fasahohi kawai zai yi ba, zai kuma kara samar da damammaki ga kamfanoni mahalarta bikin don su yi mu’amala da juna, da inganta hadin-gwiwa da samar da ci gaba tare.

Ina dalilin da ya sa kasa da kasa suka zabi kasar Sin don bullo da sabbin kayayyaki ko kuma fasahohin da suka samar karo na farko? Amsar ita ce, tattalin arzikin kasar na da karfi da kuzari, abun da ya sa kamfanonin da suke halartar bikin CIIE ke da yakinin game da kasuwar kasar Sin, da fatan samun damammakin da kasar ta ba su.

Ina dalilin da ya sa kasa da kasa suka zabi kasar Sin don bullo da sabbin kayayyakin da suka samar?_fororder_B

Babu wani kamfani da zai iya yin biris da babbar kasuwar da kasar Sin take da ita, ganin adadin mutanen da take da su da ya zarce biliyan 1.4. Har wa yau, yanayin kasuwanci na ta kyautata a kasar Sin, musamman ganin yadda gwamnatin kasar take himmatuwa wajen kare hakkin mallakar ilimi, wanda ya sa manyan kamfanonin kasa da kasa suka kudiri aniyar bullo da sabbin fasahohi da kayayyakinsu a kasuwar kasar.

A dayan bangaren ma, kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka a zahiri, wato fadada bude kofarta ga kasashen waje, abun da ya kwantar da hankalin kamfanoni daban-daban. A wajen bikin kaddamar da CIIE a wannan karo, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, babu wani abun da zai iya sauya aniyar kasarsa na habaka bude kofarta ga kasashen ketare.

A halin yanzu kasar Sin na nuna himma da kwazo wajen mayar da kasuwarta ta zama kasuwar duk duniya, a wani kokari na samar da ci gaban kasa da kasa tare. (Murtala Zhang)