logo

HAUSA

Mutane akalla 10 sun mutu sanadiyyar hare-hare a kauyukan Nijeriya

2021-11-06 17:15:40 CRI

Gwamnatin jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta ce mutane akalla 10 ne suka mutu, sanadiyyar mabanbantan hare- haren da ‘yan bindiga suka kai kauyuka biyu na jihar.

Cikin wata sanarwa, gwamnatin jihar ta ce yayin harin da ‘yan bindigar suka kai da safiyar jiya Juma’a, a kauyukan Yagbak da Unguwan Ruhugo na yankin karamar hukumar Zangon Kataf, wasu mutane da ba a san adadinsu ba sun jikkata, kana an kone gidaje.

Gwamnati ta yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu, ta ce ta samu labarin aukuwar hare-haren ne daga hukumomin soji da na ‘yan sanda.

A cewar wani ganau, ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan fashi ne, sun shiga kauyukan ne kan Babura, inda suka yi ta harbin mazauna, suna kuma cinnawa gidaje wuta.

Gwamnatin jihar ta kara da cewa, ta bada umarnin gudanar da bincike kan hare-haren da kuma samar da tallafi ga mutanen da lamarin ya rutsa da su. (Fa’iza Mustapha)