logo

HAUSA

Kwamitin sulhu na MDD ya damu da ta’azzarar rikici a arewacin Habasha

2021-11-06 17:17:08 CRI

Kwamitin sulhu na MDD ya damu da ta’azzarar rikici a arewacin Habasha_fororder_2fdda3cc7cd98d10a8cdee33b882d9077aec90da

Mambobin kwamitin sulhu na MDD, sun bayyana matukar damuwa game da ta’azzara da fadadar rikicin a arewacin Habasha.

Cikin wata sanarwa a jiya, sun bayyana tasirin rikicin kan yanayin jin kai, da kwanciyar hankalin kasar da ma yankin baki daya.

Sanarwar ta yi kira da a girmama dokar jin kai ta kasa da kasa, domin bada dama ga gudanar ayyukan agaji ba tare da wata tangarda ba, da farfado da hidimomin jama’a da kara kaimi wajen bayar da agaji.

Har ila yau, mambobin kwamitin sun yi kira da a kawo karshen rikice-rikice, suna cewa, zai iya zama mafari ga tattaunawar kasa da zata kunshi kowa da kowa, da zummar warware rikicin da shimfida tubalin zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar.

Sun kuma jaddada goyon bayansu ga rawar da hukumomi a yankin ke takawa, da suka hada da Tarayyar Afrika da kuma babban wakilinta a yankin kahon Afrika wato Olusegun Obasanjo. (Fa’iza Mustapha)