logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga bangarorin kasar Sudan su hau teburin sulhu

2021-11-06 17:14:13 CRI

Kasar Sin ta yi kira ga bangarorin kasar Sudan su hau teburin sulhu_fororder_1329049124168531978

Babban jami'in kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, Li Song, ya ce kasarsa na bibiyar yanayin da ake ciki a kasar Sudan, kuma tana kira ga dukkan bangarori su warware sabaninsu ta hanyar tattaunawa, ta yadda za a samu wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Da yake jawabi yayin wata zama ta musammam, ta yini guda ta majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD kan tasirin yanayin Sudan kan hakkin dan Adam, Li Song ya jaddada cewa, kasar Sin na nacewa ga akidar kaucewa tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe, kuma ta yi amana al’ummar Sudan na da hikimar tafiyar da harkokinsu na cikin gida yadda ya kamata.

Ya ce Sin na goyon bayan al’ummar kasar su warware matsalarsu da kansu, yana mai kira ga kasashen waje, su samar da kyakkyawan yanayin da dukkan bangarorin Sudan din za su warware sabaninsu ta hanyar tattaunawa. (Fa’iza Mustapha)