logo

HAUSA

Sama da mutane 100 ne suka mutu sanadiyyar fashewar wata tankar mai a Saliyo

2021-11-06 20:51:21 CRI

Sama da mutane 100 ne suka mutu sanadiyyar fashewar wata tankar mai a Saliyo_fororder_微信图片_20211106205000

Rundunar ‘yan sandan Saliyo, ta ce sama da mutane 100 ne suka mutu, sanadiyyar fashewar wata tankar mai a birin Freetown na Saliyo.

Hatsarin ya auku ne da yammacin jiya Juma’a, bayan tankar ta yi arangama da wata babbar mota a yankin gabashin birnin, lamarin da ya yi sanadin yoyon man fetur.

Wasu ganau sun ce mazauna yankin sun fito kwasar man fetur dake yoyo a lokacin da tankar ta fashe tare da kamawa da wuta, wanda ya rutsa da mutane da dama.

Babban jami’in sashen adana gawarwaki na asibitin Connaught na Saliyo, Sinneh Kamara, ya shaidawa Xinhua cewa, sun karbi gawarwaki 95 da safiyar yau Asabar, kuma suna fargabar za a sami karin adadin, saboda yadda wadanda aka kwantar a asibitocin dake fadin birnin Freetown, ke cikin yanayi mai tsanani. (Fa’iza Mustapha)