logo

HAUSA

Wasu kafofin Amurka da na Turai sun zargi Sin da tsaurara matakan dakile COVID-19 da nufin yi mata matsin lamba

2021-11-05 16:00:56 CRI

Wasu kafofin Amurka da na Turai sun zargi Sin da tsaurara matakan dakile COVID-19 da nufin yi mata matsin lamba_fororder_211105-推送-hoto1

Wasu kafofin watsa labarai na Amurka da wasu kasashen Turai, ciki har da “New York Times" da "Wall Street Journal" na Amurka, da "Guardian" ta Birtaniya, sun wallafa wasu sharhohi dake zargin kasar Sin, suna cewa wai ta yi matukar matsawa wajen aiwatar da matakan dakile cutar COVID-19.

Kafar World Socialist Network ce ta tabbatar da hakan cikin wata makala da ta wallafa a ran 1 ga watan nan na Nuwamba. Kafar ta ce dalilin wadancan kafofi na wallafa rahotannin shi ne, matsawa kasar Sin lamba, har sai ta rungumi manufofin kasashen yamma na yaki da annoba, wanda hakan ke kunshe da makircin siyasa.

To amma babban abun tambayar shi ne, me ya sa wadannan kasashen ke aiwatar da munanan matakai na yaki da wannan annoba, wadanda suka haifar da harbuwa da rasuwar al’ummun su masu tarin yawa. (Saminu Hassan)