logo

HAUSA

Muhimman manufofin Sin da ba sa sauyawa suna karfafa gwiwar kamfanonin kasa da kasa

2021-11-05 10:01:24 CRI

Muhimman manufofin Sin da ba sa sauyawa suna karfafa gwiwar kamfanonin kasa da kasa_fororder_211105-锐评 S1-Ruiping2

Shugaban sashen kasar Sin na kamfanin Qualcomm Frank Meng, ya ce burin kasar Sin na fadada bude kofa ga duniya ba zai taba sauyawa ba, kamar dai yadda shugaban kasar Xi Jinping ya bayyana, cikin jawabin sa na bude taron baje kolin kasa da kasa, na hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na 4.

A yawabin da shugaban na Sin ya gabatar ta kafar bidiyo da yammacin jiya Alhamis, shugaba Xi ya ce kasarsa ta sha alwashin raba damammakin ta na wanzar da ci gaba da sauran sassan duniya, tana kuma fatan ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, ta yadda zai kara zama budadde, wanda zai hade kowa, mai cike da daidaito, kana bisa tushen cin moriyar juna. Dukkanin wadannan manufofi na Sin, a cewar shugaba Xi, ba za su taba sauyawa ba.

Game da hakan, Frank Meng ya ce kalaman na shugaban kasar Sin, sun dace da manufofin da kamfanoni mahalarta baje kolin CIIE na bana suka dade suna dakon ji.

Ya ce batun tabbatar da cudanyar dukkanin sassa, da amfanar dukkanin sassa daga damammakin kasuwanni tare, da fadada bude kofa, da kare moriyar juna, na cikin manyan sassa da shugaba Xi ya tabo a jawabin nasa. Ya kara da cewa, Sin ta samu saurin bunkasar tattalin arziki cikin gwamman shekarun baya bayan nan, yayin da wasu sassan kasa da kasa ke dandana kudar su sakamakon tasirin annobar COVID-19. To sai dai kuma Sin ta amince cewa, ba za ta samu cikakken ci gaba ita kadai ba, kana sauran kasashen duniya ma ba za su cimma nasara ba tare da kasar Sin ba.

Muhimman manufofin Sin da ba sa sauyawa suna karfafa gwiwar kamfanonin kasa da kasa_fororder_211105-锐评 S1-Ruiping

A yau, Sin na da yawan al’umma sama da biliyan 1.4, kuma masu samun matsakaicin kudin shiga a kasar sun kai sama da miliyan 400, kasar tana kuma shigo da hajoji da hidimomi da suka kai darajar kusan dala tiriliyan 2.5 a duk shekara. Don haka, wanzuwar baje kolin CIIE ya kara gabatar da babbar kasuwar kasar Sin ga kamfanonin kasa da kasa.

A bana, kusan kamfanoni 3,000 daga kasashe da yankuna 127 ne suka halarci baje kolin CIIE. Kamfanonin sun fito ne daga sama da nahiyoyi 5, ciki har da na kasashe masu tasowa, da masu rangwamen wadata. Kari kan hakan, adadin kamfanoni masu karfi 500, da jagororin manyan kamfanoni da suka halarci baje kolin na bana, sun haura na wanda ya gabata, yayin da kuma adadin masu baje hajoji ya kai kaso 80%. Hakan shi ne abu mafi jan hankali game da baje kolin CIIE, baya ga kasancewarsa damar ci gaba da bude kofofin Sin ga kasuwannin duniya.

A halin da ake ciki, annobar COVID-19 na kara yin mummunan tasiri ga duniya, kana tattalin arzikin duniya na fuskantar kalubalen farfadowa. Amma a bangaren Sin, kara bude kofofin ta hanya ce mai kyau, wadda kasar za ta ci gaba da bi wajen shawo kan kalubale, da wanzar da ci gaba tare da sauran sassan duniya. A lokaci guda kuma, Sin na ci gaba da goyon bayan kasashen duniya wajen kara bude kofofin su, tana kuma adawa da matakan ware kai, da sanyawa kasuwanni shinge, kana tana fatan iskar ’yancin bude kasuwanni ga juna, za ta karade daukacin sassan duniya baki daya.  (Saminu)