logo

HAUSA

Masar ta karbi wata sabuwar gudunmawar alluran riga kafin COVID-19 na kasar Sin

2021-11-05 10:07:26 CRI

Masar ta karbi wata sabuwar gudunmawar alluran riga kafin COVID-19 na kasar Sin_fororder_211105-Masar-F1

Kasar Sin ta mika wani sabon kashi na gudunmawar rigakafin COVID-19 ga kasar Masar, a wani bangare na zurfafa hadin gwiwarsu a fannin yaki da annobar.

An gudanar da bikin mika gudunmawar a ranar Laraba, wanda ya samu halartar jakadan kasar Sin a Masar, Liao Liqiang da ministan ilimi na kasar, Khaled Abdel Ghaffar, wanda kuma shi ne ke rikon ma’aikatar lafiya ta kasar na wucin gadi.

A cewar Liao Liqiang, kawo yanzu, kasar Sin ta bayar da gudunmawar rigakafin COVID-19 ga kasar Sin har sai hudu, haka kuma ana samar da riga kafin Sinovac a Masar din, wanda ke nuna karfin dangantakar kasashen biyu wajen yaki da annobar, da kuma muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Sanarwar da ma’aikatar lafiya ta Masar ta fitar, ta ruwaito Abdel-Ghaffar na yabawa dimbin taimako da tallafin da kasar Sin ke ba Masar a yaki da annobar COVID-19. (Fa’iza Mustapha)