logo

HAUSA

Wane laifi jirgin karkashin ruwan teku na Amurka mai suna Connecticut ya aikata a yankin tekun kudancin kasar Sin?

2021-11-05 21:07:20 CRI

Wane laifi jirgin karkashin ruwan teku na Amurka mai suna Connecticut ya aikata a yankin tekun kudancin kasar Sin?_fororder_A

Rahotanni daga kafar watsa labarai ta ABC ta kasar Amurka sun nuna cewa, sakamakon hatsarin da jirgin karkashin teku na Amurka mai suna Connecticut dake amfani da makamashin nukiliya ya yi a karkashin yankin tekun kudancin kasar Sin, an tsige wasu manyan shugabannin jirgin uku. Amma game da gaskiyar hatsarin, rundunar sojan Amurka ba ta yi wani karin bayani ba, sai dai kawai ta ce jirgin ya ci karo da wani abu da ake zaton dutse ne a karkashin teku, inda ta ci gaba da yin biris da damuwar da ake nunawa, kan cewa ko hatsarin ya janyo yoyon makamashin nukiliya ko kuma a’a. Wane irin laifi jirgin na Connecticut ya aikata a yankin tekun kudancin kasar Sin? Ya kamata kasar Sin gami da kasashen dake makwabtaka da tekun kudancin kasar su san zahirin abin da ke faruwa.

Manazarta sun lura cewa, jiragen yaki masu amfani da makamashin nukiliya dake karkashin teku, muhimman makamai ne da rundunar sojan ruwan Amurka kan yi amfani da su wajen yin yake-yake a karkashin ruwa, kana, jirage ne masu leken asirin karfin rundunonin soja na wasu kasashe. Saboda haka, akwai wasu kwararru a fannin aikin soja da suke ganin cewa, akwai yiwuwar jirgin karkashin ruwa na Amurka mai suna Connecticut ya gudanar da aikin leken asiri ne a yankin tekun kudancin kasar Sin, al’amarin da ya sa rundunar sojan Amurka ta boye wasu abubuwa game da gaskiyar hatsarin.

Wane laifi jirgin karkashin ruwan teku na Amurka mai suna Connecticut ya aikata a yankin tekun kudancin kasar Sin?_fororder_B

Har wa yau, wani abu da ya kara janyo damuwar kasa da kasa shi ne, yiwuwar hadarin yoyon makamashin nukiliya. Kwararru a fannin aikin soja sun bayyana cewa, idan har jirgin dake amfani da makamashin nukiliya ya yi hatsari a karkashin teku, to akwai yiwuwar hakan zai iya haddasa gurbatar nukiliya. Kuma idan da gaske jirgin Amurka ya ci karo da wani dutse a teku, hakan na iya kara haddasa hadarin.

Tekun kudancin kasar Sin, muhalli ne na dukkan kasashen dake wannan yanki, wanda bai kamata ya zama wajen da Amurka take yunkurin neman cimma muradun siyasa ba. Game da rashin kulawa da yaudarar da Amurka ta yi, ya zama dole kasar Sin da sauran wasu kasashen dake wannan yanki su binciki gaskiyar lamarin, su kuma bukaci Amurka ta biya diyya, don kare hakkin al’ummomin duniya baki daya. (Murtala Zhang)