logo

HAUSA

Gwamnan jihar Lagos ya ayyana zaman makoki na kwanaki 3 don jimamin wadanda suka mutu a ginin da ya rufta

2021-11-05 20:32:41 CRI

Gwamnan jihar Lagos ya ayyana zaman makoki na kwanaki 3 don jimamin wadanda suka mutu a ginin da ya rufta_fororder_b03533fa828ba61ef59a25d75d40f703314e594b

Gwamnan jihar Lagos a tarayyar najeriya Babajide Sanwo-Olu, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku, biyo bayan rugujewar wani gini da ya yi sanadin mutuwar mutane a ranar Litinin da yamma a cibiyar tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis cewa, za a sassauto da dukkan tutoci dake cikin gine-ginen gwamnati da na sassa masu zaman kansu zuwa kasa-kasa, tare da soke ayyukan hukuma a lokacin zaman makoki. Ya bayyana cewa, za a fara zaman makokin ne a yau Juma’a a kuma kare ranar Lahadi.

Ya zuwa jiya Alhamis, adadin wadanda suka mutu sakamakon ruftawar ginin a unguwar Ikoyi da ke Lagas, ya karu zuwa 38, bayan da masu aikin ceto suka zakulo wasu gawarwaki daga cikin baraguzan ginin, kamar yadda jami’in tsare-tsare na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa a jihar Legas, Ibrahim Farinloye ya bayyana.