Yusuf Ibrahim: Ya dace a koyi darussa daga matakan kasar Sin na yaki da cutar COVID-19
2021-11-09 14:51:56 CRI
Yusuf Ibrahim, dalibi dan asalin jihar Kogin tarayyar Najeriya ne wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a jami’ar nazarin harkokin man fetur dake yankin Changping na birnin Beijing. A yayin zantawar da ya yi da Murtala Zhang, malam Yusuf Ibrahim, wanda ya yi shekaru biyu yana karatu da rayuwa a kasar Sin, musamman birnin Beijing, ya bayyana ra’ayinsa kan bambancin yanayin karatu tsakanin gida Najeriya da kasar Sin, da kuma matakan kandagarkin cutar mashako ta COVID-19 da gwamnatin kasar Sin take dauka.
Har wa yau, malam Yusuf ya ce yana fatan amfani da ilimin da ya samu a kasar Sin don bada gudummawarsa wajen karfafa zumunta tsakanin Najeriya da China. (Murtala Zhang)