logo

HAUSA

Baje kolin CIIE ya zama dandalin karfafa manufar kasar Sin ta kara bude kofa ga waje

2021-11-04 18:28:30 cri

Baje kolin CIIE ya zama dandalin karfafa manufar kasar Sin ta kara bude kofa ga waje_fororder_wc930x592_09fb96a45c744db081ca8c5cfaea00cb

Yayin da kamfanoni masu baje kolin hajoji kusan 3,000, daga kasashe da yankuna 127 suka hallara a birnin Shanhai na kasar Sin, domin halartar bikin baje kolin kasa da kasa na hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE a takaice, masharhanta na kallon baje kolin a matsayin wani dandali dake kara fayyace manufar kasar Sin ta bude kofa ga waje, yayin da ake tunkarar sabbin kalubale na farfadowar tattalin arzikin duniya.

Duk da matsalolin da duniya ke fuskanta game da farfadowa, da raya ayyukan masana’antu, kamfanoni da sassan masu ruwa da tsaki sun hallara, domin cin gajiya daga kyakkyawan yanayin raya cinikayya, da kulla yarjeniyoyin hadin gwiwar kasuwanci. A hannu guda kuma, baje kolin ya baiwa manyan kamfanoni, da masana’antu da suka yi fice a fannin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, damar baje sabbin fasahohin su domin cin gajiyar daukacin bil adama.

Wasu sassan baje kolin CIIE dake jan hankalin al’ummar duniya a bana, sun hada da fannin kirar ababen hawa masu amfani da makamashi mai tsafta. Akwai kuma fannin na’urorin laturoni na zamani, da na tsaftace ruwa, da na’urorin samar da kariya ga rayukan bil adama. Sauran sun hada da na sabbin fasahohin kiwon lafiya, da na kare muhallin halittu da muhallin bil adama, da sabbin na’urorin dake iya taimakawa wajen rage fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi.

Ko shakka babu, baje kolin CIIE baya ga kasancewarsa wata gada ta kara sada kasar Sin da sauran sassan duniya a bangarorin kirkire kirkiren kimiyya da fasaha, a hannu guda kuma, yana kara fito da gudummawar kasar Sin a fannin wanzar da ci gaban tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)