logo

HAUSA

Kamfanonin Afrika ta kudu za su baje hajojinsu yayin bikin baje koli na nahiyar Afrika

2021-11-04 10:56:47 CRI

Kamfanonin Afrika ta kudu za su baje hajojinsu yayin bikin baje koli na nahiyar Afrika_fororder_211104-faiza-3-South Africa

Jimilar kamfanoni 80 na kasar Afrika ta kudu ne za su baje hajoji da hidimominsu yayin baje kolin nahiyar Afrika na 2021, domin shiga kasuwannin nahiyar.

Ma’aikatar kula da cinikayya da masana’antu da takara na kasar, ta ce baje kolin zai ba masu saye da sayarwa da zuba jari, damar musayar bayanai da damarmakin zuba jari da za su taimakawa bikin baje kolin.

Baje kolin na bana zai gudana ne a birnin Durban na lardin KwaZulu-Natal, daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Nuwamba.

Frimiyan yankin KwaZulu-Natal, Sihle Zikalala, ya ce ya shirya tarbar wakilai da jami’an harkokin kasuwanci da masu baje koli da sayar da kayayyaki yayin bikin baje kolin. (Fa’iza Mustapha)