logo

HAUSA

Me sojojin Amurka suke neman boyewa a batun hatsarin jirginsu mai amfani da makamashin nukiliya a karkashin teku?

2021-11-04 20:48:20 CRI

Me sojojin Amurka suke neman boyewa a batun hatsarin jirginsu mai amfani da makamashin nukiliya a karkashin teku?_fororder_A

Kwanan nan ne rundunar sojan Amurka ta fitar da rahoton binciken hatsarin da jirginsu mai amfani da makamashin nukiliya ya yi, inda ya yi mummunar lalacewa bayan da ya ci karo da wani dutse a karkashin teku. Amma rahoton bai ambaci komai ba game da ainihin makasudin tafiyar jirgin a karkashin teku, da inda hatsarin ya wakana, haka kuma bai yi bayani filla-filla kan wasu muhimman batutuwa ba, ciki har da ko hatsarin ya janyo yoyon makamashin nukiliya ko a’a, ko hatsarin ya kawo illa ga muhallin halittun yankin tekun kudancin kasar Sin ko a’a. Tambayar ita ce, mene ne sojojion Amurka suke kokarin boyewa?

Na farko, me ya kawo jirgin Amurka mai suna Connecticut wurin? Manazarta na ganin cewa, lokacin da ake kara samun ja-in-ja tsakanin Sin da Amurka, jirgin ya shigo yankin tekun kudancin kasar Sin ne don leken asirin soja. Har ma wasu na shakkun cewa, sau nawa jiragen karkashin teku na Amurka suka shigo yankin tekun kudancin kasar Sin?

Na biyu, shin hatsarin jirgin ya janyo yoyon makamashin nukiliya? Abun lura a nan shi ne, bayan abkuwar hatsarin, ayarin jiragen ruwan yaki na Amurka dake tekun Pasifik ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce hatsarin bai kawo illa ga na’urar dake samar da karfin nukiliyar jirgin ba. Amma abun mamaki a nan shi ne, kwanan nan sojojin Amurka sun taba tura jiragen saman yakinta zuwa yankin tekun kudancin kasar Sin don gudanar da bincike. Kuma jaridar SCMP ta yankin Hong Kong na kasar Sin ta yi kiyasin cewa, makasudin yin haka shi ne domin binciken ko hatsarin jirgin ya yi sanadin yoyon makamashin nukiliya ko a’a.

Me sojojin Amurka suke neman boyewa a batun hatsarin jirginsu mai amfani da makamashin nukiliya a karkashin teku?_fororder_B

Hatsarin jirgin Connecticut ya sake shaidawa duniya yadda sojojin Amurka suke nuna babakere da danniya bisa hujjar “samun ‘yancin yin zirga-zirga a yankin teku”, kuma ita Amurka din kasa ce dake yunkurin rura wutar rikicin soja a yankin tekun kudancin kasar Sin, kana shi ne babban dalili da ya lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Kamata ya yi sojojin Amurka su baiwa duniya amsa mai gamsarwa, game da shakkun da ake nunawa kan hatsarin jirgin nata! (Murtala Zhang)