Sin: rahoton da ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar na cike da son zuciya
2021-11-04 21:10:24 CRI
Dangane da sabon rahoton da ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar kan karfin sojan kasar Sin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin, ya mayar da martani a gun taron manema labarai da aka saba gudanarwa Alhamis din nan cewa, rahoton na ma'aikatar tsaron Amurka, kamar irin rahotannin da ta saba fitarwa a baya, ya yi watsi da gaskiya, kuma yana cike da bayanai na son zuciya. Bangaren Amurka ya yi amfani da rahoton, wajen yada dabarar barazanar nukiliyar kasar Sin, wata dabara ce kawai ta sarrafa kalmomi da rudar da mutane, kuma al'ummar duniya suna sane da hakan.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, a hakikanin gaskiya, Amurka ce kasa mafi girma a duniya wajen fuskantar barazanar nukiliya. Don haka, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta dage wajen daukar nauyin da ya rataya a wuyanta na musamman, na kawar da makaman nukiliya daga doron duniyarmu, da kara rage yawan makaman nukiliyarta, da kiyaye daidaito da kwanciyar hankali a duniya.