logo

HAUSA

Iran da EU za su koma tattaunawa game da yarjejeniyar JCPOA

2021-11-04 10:19:37 CRI

Iran da EU za su koma tattaunawa game da yarjejeniyar JCPOA_fororder_211104-saminu-3-Iran Nuclear

Babban mai shiga tsakani na gwamnatin Iran game da batun nukiliyar kasar Ali Bagheri Kani, ya ce kasar sa da kungiyar tarayyar turai ta EU, za su koma teburin shawarwari game da yarjejeniyar nukiliyar Iran din ta shekarar 2015 ko JCPOA a takaice.

Ali Bagheri Kani, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, ya ce za a koma tattaunawar ce ta birnin Vienna a ranar 29 ga watan nan na Nuwamba. Jami’in wanda ya bayyana hakan bayan tattaunawa da mataimakin babban sakataren kungiyar EU mai lura da harkokin waje Mr Enrique Mora, a biranen Tehran da Brussels, ya ce Iran da EU sun cimma matsaya game da komawa teburin shawara.

Ya ce Iran ta amince cewa, batun dage takunkumin da aka kakaba mata, da wajibcin aiwatar da dukkanin hakkokin dake rataye a wuyan sassa masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar ta JCPOA, su ne manyan ajandojin da za a tattauna, yayin shawarwarin da aka jingine tun watan Yuni, bayan sauyin matsalar gwamnatin Iran. (Saminu)