logo

HAUSA

An kashe mahara 6 a yammacin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

2021-11-04 10:41:30 CRI

An kashe mahara 6 a yammacin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo_fororder_211104-faiza-2-South Kivu

Wani gungun ’yan tawaye ya kai hari wurare da dama dake birnin Bukavu na gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ciki har da sansanonin soji.

Gwamnan Kivu ta Kudu, Theo Kasi, ya bayyana yayin taron majalisar tsaron yankin cewa, yayin harin da ya auku da misalin karfe 1:40 na tsakar daren ranar Laraba, jami’an tsaro sun kashe mahara 6, yayin da sojoji 2 suka rasa rayukansu.

A cewar Gwamnan, jimilar mahara 36 aka kama, yana mai cewa ana gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu cikin lamarin.

Shugaban rundunar soji na Kivu ta Kudu Bob Kilubi, ya dora alhakin harin kan kungiyar ’yan tawaye da ake kira “CPC 64”. ’Yan tawayen sun yi yunkurin sakin ’yanuwansu da ’yan sandan Bukavu ke rike da su tun cikin makon da ya gabata. (Fa’iza Mustapha)