logo

HAUSA

Kungiyar AU ta sha alwashin tallafawa ayyukan wanzar da zaman lafiya tsaro da bunkasa ci gaba

2021-11-04 10:05:50 CRI

Kungiyar AU ta sha alwashin tallafawa ayyukan wanzar da zaman lafiya tsaro da bunkasa ci gaba_fororder_211104-saminu-2-AU

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta sha alwashin tallafawa ayyukan wanzar da zaman lafiya, tsaro da bunkasa ci gaba a sassan nahiyar Afirka, a wani mataki na wanzar da ci gaba.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin wani taro a birnin Nairobin kasar Kenya, kwamishina mai lura da harkokin siyasa da tsaro na kungiyar Bankole Adeoye, ya ce AU ta tsara wani shiri na samar da gargadin gaggawa, da nufin dakile tashe tashen hankula daga tushe. Ya kuma ja hankalin gwamnatoci da su magance dalilan dake haifar da rashin kwanciyar hankali a shiyyar.

Jami’in na AU ya lura cewa, raunin jagoranci, da yaduwar kananan makamai, tare da karancin guraben ayyukan yi tsakanin matasa, na kan gaba wajen haifar da rashin zaman lafiya a nahiyar.

Bankole Adeoye ya kara da cewa, AU ba za ta taba lamuntar sauyin gwamnati ta hanyoyin da suka sabawa kundin tsarin mulki a sassan nahiyar ba.  (Saminu)