logo

HAUSA

Masu rajin ci gaban Afrika sun bukaci a samar da kudaden sauyin yanayi da sassauta basuka don gina makoma mai kyau

2021-11-03 10:49:56 CRI

Masu rajin ci gaban Afrika sun bukaci a samar da kudaden sauyin yanayi da sassauta basuka don gina makoma mai kyau_fororder_1103-Afirka-Climate-Ahmad

Gamayyar masu fafutukar kawo ci gaba sun bukaci kasashen duniya su cika alkawurransu na samar da kudaden tallafawa shirin yaki da sauyin yanayi a Afrika tare da saukaka basuka a matsayin hanyar samar da yanayin ci gaba mai tsafta da kuma kyautata makomar bunkasuwar nahiyar.

A jawaban da suka gabatar a gefen taron kolin sauyin yanayi na MDD karo na 26, (COP26) wanda ke gudana a Glasgow na Scotland na kasar Birtaniya, masu rajin kawo cigaban sun jaddada cewa, samar da isassun kudade, da fasahohin zamani, kana da sassauta basuka na daga cikin matakan da za su taimaka wajen gaggauta farfadowar ci gaba mai tsafta a nahiyar daga wahalhalun da take fuskanta sakamakon matsalolin tsananin dumamar yanayi.

Mithika Mwenda, babban daraktan kungiyar gamayyar yaki da sauyin yanayi ta Afrika PACJA, dake da ofishinta a Nairobi, ya bayyana cewa, nahiyar ta cancanci samun kason kudaden yaki da sauyin yanayi bisa adalci, da musayar fasahohi, da yafe basuka domin ta samu damar bunkasa shirin rage fitar da hayakin dake gurbata muhalli.

Mwenda ya ce, "bukatunmu na musamman da kuma yanayin da muke ciki a matsayin nahiyar dake cike da matsalolin sauyin yanayi mun cancanci samun kulawa.” (Ahmad Fagam)