logo

HAUSA

Matakan kasar Sin na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhallin duniyarmu

2021-11-03 09:10:33 CRI

A kwanakin baya ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani mai taken "Daukar mataki kan sauyin yanayi: Manufofin kasar Sin da ayyukanta” domin adana irin ci gaban da kasar ta samu wajen dakile matsalar sauyin yanayi, da kuma raba gogewarta da hanyoyin da take bi wajen magance wannan matsala da sauran kasashen duniya. A daidai lokacin da shugabannin duniya ke taro kan sauyin yanayi a birnin Glasgow.

Matakan kasar Sin na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhallin duniyarmu_fororder_211103世界21041-hoto2

A cewar takardar bayanin, kasar Sin ta daidaita matsalar gurbata muhalli, da rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, da sa kaimi ga samarwa da kuma amfani da makamashi maras gurbata muhalli, da sauyawa ga masana'antu da ba sa fitar da iskar Carbon mai yawa, da kara karfin muhallin halittu na iya nutsar da iskar carbon, da inganta rayuwa ba tare da gurbata muhalli ba da rage fitar da iskar carbon.

Takardar ta kara da cewa, magance sauyin yanayi, shi ne abin da dukkan bil-adama suka yi amana a kai. Don haka, takardar ta yi kira ga kasashen duniya, da su himmatu wajen samar da ci gaba mai dorewa, da ra'ayin kasancewar bangarori daban-daban, da manufar bai daya amma bisa banbancin ra'ayi, da hadin gwiwar moriyar juna, da daukar matakai na zahiri.

Matakan kasar Sin na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhallin duniyarmu_fororder_211103世界21041-hoto4

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su karfafa matakan hadin gwiwar shawo kan kalubalen sauyin yanayi, cikin wata wasika da ya aike ga taron shugabannin duniya na 26 dangane da sauyin yanayi mai lakabin COP26, dake gudana a birnin Glasgow, inda ya gabatar da wasu shawarwarin guda 3. Da farko ya ce kamata ya yi a rungumi manufar cudanyar sassa daban daban, tare da maida hankali ga aiwatar da matakai na hakika, da gaggauta karkata ga amfani da makamashi mara gurbata yanayi.

Ya kuma jaddada nauyin dake wuyan kasashe masu wadata, wadanda ya ce baya ga bukatar kara fadada kwazon su, ya dace su kuma samar da tallafi ga kasashe masu tasowa, ta yadda su ma za su samu karin nasarori a wannan fanni.

Matakan kasar Sin na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhallin duniyarmu_fororder_211103世界21041-hoto3

Daga nan sai ya karfafa muhimmancin karkata ga amfani da makamashi mara gurbata yanayi, inda ya ce kamata ya yi a yi amfani da kirkire kirkiren kimiyya da fasaha, wajen sauya akala, da daga matsayin amfani da makamashi da albarkatu, tare da yanayin ayyukan masana’antu daidai da burin da aka sa gaba.

Ya ce bisa burin wanzar da yanayin daidaito tsakanin rayuwar mutane da sauran halittu, Sin za ta ci gaba da dora muhimmanci ga batun kare muhallin halittu, da fadada amfani da makamashi mai tsafta, da rage fitar da iskar carbon yayin da ake aiwatar da harkokin samar da ci gaba.  (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)