logo

HAUSA

An Fahimci Sirrin Kasar Sin Na Yin Kirkire-kirkire Ta Hanyar Ba Da Lambobin Yabo Na Kimiyya Da Fasaha

2021-11-03 21:47:24 cri

An Fahimci Sirrin Kasar Sin Na Yin Kirkire-kirkire Ta Hanyar Ba Da Lambobin Yabo Na Kimiyya Da Fasaha_fororder_微信图片_20211103212337

A yau Laraba ne aka gudanar da taron mika lambobin yabo na kimiyya da fasaha na shekarar 2020 a nan birnin Beijing. Yayin bikin, an zabi ayyuka 264, da kwararru a fannin kimiyya da fasaha 10, da kungiyar kasa da kasa 1. Cikin wadanda suka samu lambar karramawar, akwai masanin ilimin kimiyya Gu Songfen, mai shekaru 91 da haifuwa, kana babban jami'in kera jirgin sama na sabuwar kasar Sin, da mashahurin masanin kimiyyar makamashin nukiliya Wang Dazhong, mai shekaru 86 a duniya, sun lashe lambobin yabo mafiya daraja a fannonin kimiyya da fasaha ta kasa. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da kansa ne ya ba su lambobin yabon.

Kirkire-kirkire shi ne matsayin farko dake jagorantar ci gaban kasar Sin. Jerin sunayen alkaluman kirkire-kirkire na duniya na shekarar 2020 ya nuna cewa, matsayin kasar Sin a fannin ya yi saurin karuwa daga na 29 a shekarar 2015 zuwa 14 a yanzu.

Kwararru ginshiki ne na ci gaban kasa. A halin yanzu, kasar Sin ita ce kasa mafi girma a duniya da ke da albarkatun kwararru a dukkan fannoni, da kuma wasu manyan fannoni na zamani da dama, yawan masana a fannin kimiyya na kasar Sin ya karu cikin sauri, har ma ya kai sahun gaba a duniya.

Ta hanyar ba da lambobin yabo na kimiyya da fasaha na kasar Sin, abu ne mai sauki a gano cewa, sirrin kasar Sin na cimma nasarori ta fuskar kirkire-kirkire, shi ne ba wai kawai kasar ta mayar da hankali da kokarin horar da kwararru a fannonin kimiyya da fasaha ba, har ma tana bude kofa ga kasashen ketare a fannin yin musanyar bayanan kimiyya da fasaha, bugu da kari ko da yaushe tana tsayawa kan ra’ayinta na “Ci gaban kimiyya da fasaha domin kyautata rayuwar dukkan bil'adama, da karfafa ilmi da hikimar al'ummar bil'adama. Wannan ya kara shaida ra’ayin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam, kuma ya kasance muhimmiyar gudunmawar da kasar Sin mai kirkire-kirkire ta bayar ga duniya. (Mai fassara: Bilkisu)