logo

HAUSA

Beijing 2022: Kasar Sin Ta Shirya Nunawa Duniya Gasa Mai Armashi Da Kiyaye Muhalli

2021-11-03 16:52:25 CRI

Beijing 2022: Kasar Sin Ta Shirya Nunawa Duniya Gasa Mai Armashi Da Kiyaye Muhalli_fororder_111

Yanzu haka kasar Sin ta shirya tsaf don karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta shekarar 2022, wanda birnin Beijing zai karbi bakunci. Birnin Beijing dai shi ne birnin na farko da ya taba karbar bakuncin gasar wasannin Olympics guda biyu, wato na lokacin zafi a shekarar 2008 da kuma na lokacin hunturu dake tafe.

Sanin kowa ne cewa, tuni wutar gasar Olympics ta birnin na Beijing ta iso nan kasar Sin daga birnin Athens na kasar Girka, inda daga bisani aka gudanar da bikin maraba da zuwanta a filin wasanni na hasumiyar Olympics dake kusa da babban filin wasa na kasa, wurin da aka gudanar da bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi a shekarar 2008.

An kunna wutar gasar ce a wani salon bikin gargajiya da ya gudana a tsohon filin wasan Olympia dake yammacin kasar Girka, daga nan ne kuma aka mika wutar ga masu shirya gasar ta birnin Beijing dake tafe a farkon shekarar 2022 mai zuwa, a filin wasa na Panathenac dake Athens.

Bayanai na nuna cewa, kwamitin shirya gasar ta lokacin hunturu ta Beijing ta shekarar 2022, ya riga ya fitar da rigunan aiki na gasar da na ajin nakasassu a hukumance, inda aka yi kiyasin cewa, sama da mutane 30,000 ne za su yi amfani da rigunan daga sassan duniya. An kuma tsara al’adun kasar Sin da al’adun kwazon Sinawa a jikin rigunan, baya ga samfuran lambobin yabon gasar.

Kawo yanzu an kammala girke dukkan na’urorin zamani masu inganci da za a watsa gasar kai tsaye ga duniya da aikin shirya dakin gwaji a wurare uku da za a shirya gasar wato, cikin garin birnin Beijing da yankin Yanqing dake karkarar birnin Beijing da kuma birnin Zhangjiakou na lardin Hebei. Wannan ya kara tabbatar da aniyar kasar Sin ta cika alkawarinta game da shirya wannan gasa kamar yadda aka tsara, bisa tsauraran matakan kandagarki da dakile yaduwar annobar COVID-19 ba kuma tare da gurbata muhalli ba.

Duk a kan wannan gasa dake daukar hankali duniya yanzu haka, kwanan baya, gwamnatoci da kwamitocin shirya gasar wasannin Olympics na kasashe da dama, sun bayyana fata da goyon bayansu ga gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi da birnin Beijing na kasar Sin zai karbi bakunci, kana wasu ofisoshin jakadanci dake kasar Sin ma, sun gudanar da shagulgula masu jigon wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing.

Masu fashin baki na cewa, shirye-shiryen wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing na shekarar 2022, sun janyo hankali da goyon baya daga al'ummomin duniya matuka, bisa la’akari da sanarwar bayan taron kolin Rome da shugabannin G20 suka fitar, inda suka bayyana fatansu game da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da ajin nakasassu, tare da imanin cewa, wannan wata muhimmiyar dama ce ga ’yan wasa daga ko ina cikin duniya za su fafata, kana wata alama ce ta juriyar dan Adam.

Birnin Beijing dai ya dauki harami, ita ma kasar Sin ta shirya tsaf, don karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, inda take fatan farfado da sha'awar gasar Olympics da burin jama'ar duniya, wajen shirya gasar wasannin Olympic cikin sauki, aminci da ban sha'awa da al’ummar duniya za su iya kalla ta fasahohin sadarwa na zamani da ba a taba ganin irinsu ba a duniya, duk da irin nakasun da annobar COVID-19 ta haifar wajen rage armashin gasar. Rana dai ba ta karya… (Ibrahim Yaya)