logo

HAUSA

Akwai Bukatar Daukar Matakai Don Tinkarar Sauyin Yanayi

2021-11-02 22:06:28 cri

Akwai Bukatar Daukar Matakai Don Tinkarar Sauyin Yanayi_fororder_微信图片_20211102215227

"Kiyaye ra’ayin bai daya da aka cimma tsakanin bangarori da dama", "Mayar da hankali kan daukar matakai masu inganci", da "Kara saurin raya masana’antu marasa gurbata muhalli ", sune shawarwari guda uku da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar game da yadda za a tinkari sauyin yanayi, a yayin da yake gabatar da jawabi a gun taron kolin na COP26 game da Yarjejeniyar Tsarin Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a jiya Litinin.

"Daukar matakai" kalma ce mai mahimmanci a cikin shirin kasar Sin. "Sai dai fatan daukar matakai tana iya zama gaskiya". Babban dalilin da ya sa kasar Sin ta ke kara yin kira kan wannan batu, shi ne tinkarar sauyin yanayi.

"Ra’ayin kasancewar bangarori da dama hanya ce mai kyau", wannan shawarar da shugaba Xi ya gabatar ta ba da ka'idoji don tinkarar sauyin yanayi a duniya. Don haka, ya kamata bangarori daban daban su martaba "Yarjejeniyar Tsarin Sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya" da "Yarjejeniyar Sauyin Yanayi ta Paris", da kuma nacewa kan daukar "nauyi daban daban da ke bisa wuyan ko wanensu." Musamman kasashe masu ci gaba ba kawai su kara yin aiki da kansu ba, har ma da bayar da tallafi ga kasashe masu tasowa, wannan shi ne abu mai muhimmanci wajen tinkarar sauyin yanayi yadda ya kamata.

Shin ko tinkarar sauyin yanayi zai kawo tasiri ga ci gaban tattalin arziki? Xi Jinping ya ba da shawarar "hanzarta raya masana’antu masu kiyaye muhalli", da kuma ciyar da tattalin arziki da al’umma gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha.

Tinkarar sauyin yanayi kalubale ne da duk duniya ke fuskanta, don haka, akwai bukatar kasashen duniya su dauki matakai na bai daya. (Mai fassara: Bilkisu)