logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sakamakon rugujewar wani gini a Najeriya ya karu zuwa 6

2021-11-02 21:10:15 CRI

Adadin wadanda suka mutu sakamakon rugujewar wani gini a Najeriya ya karu zuwa 6_fororder_94cad1c8a786c917d991ef65f8e42cc63ac7573a

Rahotanni daga Najeriya na cewa, yawan mutanen da suka mutu sakamakon rushewar wani bene mai hawa 21 da ake ginawa a birnin Lagos, cibiyar tattalin arzikin Najeriya a ranar Litinin, ya karu zuwa shida ya zuwa ranar Talata, yayin da hukumomi suka tsananta bincike da aikin ceto.

Jami’in hukumar ayyukan bayar da agajin gaggawa ta kasa reshen jihar Lagos (NEMA) Ibrahim Farinloye, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wurin da hadarin ya faru cewa, ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a ginin da ya ruguje a unguwar Ikoyi da ke Legas, duk da ruwan sama da iska da aka yi ta samu a daren jiya

Ya ce, ba a san abin da ya haddasa rugujewar ginin ba, amma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an shafe sama da shekara guda ana wannan gini.