logo

HAUSA

CIIE na taka muhimmiyar rawa wajen fadada fitar da kayayyakin musamman na Afirka ta kudu zuwa kasar Sin

2021-11-02 21:12:06 cri

CIIE na taka muhimmiyar rawa wajen fadada fitar da kayayyakin musamman na Afirka ta kudu zuwa kasar Sin_fororder_QQ图片20211102205606

Kasar Afirka ta kudu ita ce babbar abokiyar cinikayyar kasar Sin a nahiyar Afirka. Taron baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE a takaice, ya taka muhimmiyar rawa wajen fadada fitar da kayayyakin musamman na kasar Afirka ta kudu zuwa kasar Sin. A yayin bikin na baya, adadin kudin da ya shafi kwangilolin da kamfanonin Afirka ta Kudu suka rattabawa hannu, sun kai sabon matsayi. A bana, kamfanonin Afirka ta Kudu sun sanya hannu cikin himma don halartar bikin CIIE karo na 4.

A kwanan baya, mashawarcin sashen tattalin arziki da kasuwanci na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Afirka ta Kudu mista Zhao Zhongyi ya yi bayani game da yanayin da ake ciki yayin wata hira ta musamman da ya yi da wakiliyar CMG, inda ya ce,

“A bana, sha'awar kamfanonin Afirka ta Kudu ta halartar bikin CIIE tana nan ba ta sauya ba. Alkaluman da ofishin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su a kasar Sin, sun nuna cewa, kamfanoni 16 daga Afirka ta Kudu ne suka yi rajistar shiga bikin, a filin da ya kai murabba'in mita 1,596. Wasu sanannun kamfanonin Afirka ta Kudu da yawa sun sanya hannu don shiga baje kolin, kuma ana cike da imanin cewa, za su iya samun karin oda a yayin CIIEn na wannan karo.”

Baya ga haka, Zhao Zhongyi ya kara bayyana cewa, a matsayinsa na bikin baje kolin kasa da kasa dake dora muhimmanci kan shigo da kayayyaki daga kasashen waje na farko a duniya, bikin CIIE wani babban mataki ne da kasar Sin ta dauka, na nuna goyon baya ga 'yantar da harkokin ciniki da dunkulewar tattalin arzikin duniya waje daya, da kara bude kasuwarta ga duniya, wanda ya samar da wani dandalin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa don gudanar da cinikayya, kana ya zama wani muhimmin dandali na zurfafa hadin kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka ta Kudu. (Mai fassara: Bilkisu)