logo

HAUSA

Wakilin MDD: Ana kokarin sulhunta rikicin Sudan

2021-11-02 09:47:02 CRI

Jiya Litinin, manzon musamman MDD kan batun kasar Sudan Volker Perthes, ya bayyana a birnin Khartoum fadar mulkin Sudan cewa, bangarori daban-daban da abin ya shafa, suna kokarin sulhuntawa, da shiga tsakani kan rikicin siyasa da ya barke a kasar.

A cewarsa, masu gudanar da shawarwari na neman a dauki matakin gaggawa, don kawo karshen rikicin, da sauya halin da ake ciki na rikon kwarya.

Ya zuwa yanzu, MDD ta taka rawar gani wajen shiga tsakani a rikicin Sudan, inda ta ba da tabbaci ga shawarwari tsakanin bangarori daban-daban. Volker Perthes ya ce, majalisar na tuntubar mutane dake da matsayi daban-daban a kasar, cikinsu har da wadanda basu son majalisar ta shiga tsakani, ko ba su son dawowar hadin kan sojoji da fararen hula. (Amina Xu)