logo

HAUSA

Daukar hakikanan matakai muhimmin abu ne ga kungiyar G20 wajen tinkarar kalubale

2021-11-01 20:46:35 cri

Daukar hakikanan matakai muhimmin abu ne ga kungiyar G20 wajen tinkarar kalubale_fororder_微信图片_20211101204416

“Kasashen duniya na kara nuna fata da kokari wajen tinkarar kalubale tare, yayin da abu mai muhimmanci shi ne daukar matakai a zahiri.” Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana haka ne a daren jiya yayin da yake halartar taron kolin shugabannin kungiyar G20 karo na 16 ta kafar bidiyo daga nan Beijing.

Sauyin yanayi da makamashi, sune manyan kalubale da har yanzu ake fuskanta a duniya. Jama’a sun ga cewa, duk da karuwar aniyar kasashen duniya na yin hadin gwiwa don tinkarar kalubale, amma wasu kasashe na da matsayi da bukatu daban-daban, yayin da ake tinkarar kalubalen duniya, su kan yi kira ne kawai amma ba tare da daukar matakai na hakika ba.

Dangane da batun sauyin yanayi, kasar Sin ta kasance mai fafutuka. Wata takardar bayanin da aka fitar kwanan nan, mai taken "Manufofin kasar Sin da matakan da ta dauka don tinkarar sauyin yanayi" ta yi bayani kan ci gaba da nasarorin da kasar Sin ta samu kan sauyin yanayi a 'yan shekarun nan. A gun taron kolin na Rome, kasar Sin ta sake nanata kokarinta na cimma kololuwar iskar Carbon nan da shekarar 2030 da kuma kawar da gurbatacciyar iska nan da shekarar 2060. Wannan yana nufin cewa, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin za ta kammala rage yawan iskar Carbon cikin kankanin lokaci a duniya.

A yayin taron G20 da aka shirya a Rome, an bude taron sauyin yanayi na MDD karo na 26 (COP26) a birnin Glasgow na Scotland na kasar Burtaniya. Gaba daya ana sa ran kasashen duniya, musamman ma kasashe masu ci gaba, za su cika alkawurran da suka dauka na tinkarar matsalar sauyin yanayi, da kara ba da goyon baya ga kasashe masu tasowa. Bisa wannan yanayin da ake ciki, shawarar da kasar Sin ta gabatar ta "abu mai muhimmanci shi ne a dauki matakai na hakika" shi ne mafi dacewa. (Bilkisu)