logo

HAUSA

Najeriya ta ce ta kashe 'yan ta'adda 37 a wani samame da sojoji suka yi

2021-11-01 21:19:51 CRI

Rundunar sojin Najeriya, ta ce an kashe a kalla ‘yan ta’adda 37 tare da jikkata wasu da dama, a wani samame da aka kai a karshen mako a yankin arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasar, Onyema Nwachukwu ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Litinin din nan, ya ce sojojin Operation Hadin Kai, sun lura da sanyin safiyar Asabar din da ta gabata cewa, mayakan tsageru da dama a cikin wasu manyan motoci masu dauke da bindigogi guda shida, sun kaura zuwa dajin Sambisa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, daga baya kuma suka koma wani kungurumin daji, inda suka hadu da wasu ‘yan ta’addan, a wani abu da ake ganin kamar suna kokarin yin wani taro ne.

Nwachukwu ya ce, sojojin sun lura cewa, mayakan Boko Haram da na kungiyar (ISWAP) sama da 50 ne suka hadu a wajen taron. Ya kara da cewa, rundunar ta tura jiragen sama guda biyu, domin su kai farmaki ta sama a wurin, bayan da a zahiri sun gano maboyan ‘yan ta’addan.