logo

HAUSA

An Bude Bikin Nune-nunen Fim Da Wasan Kwaikwayo Da Gasar Kacici-kacici Na Kasar Sin A Afirka

2021-11-01 16:33:40 CRI

An Bude Bikin Nune-nunen Fim Da Wasan Kwaikwayo Da Gasar Kacici-kacici Na Kasar Sin A Afirka_fororder_1101-03

A yau ne, aka gabatar da wasan kwaiwayo mai suna “wannan iyali a wancan birni” na harshen Turanci a gidan telebijin na kasar Zambia, wannan ya shaida cewa, an bude bikin nune-nunen fim da wasan kwaikwayo na kasar Sin a Afirka da gasar kacici-kacici wato The Bond karo na biyu a hukumance. Za a gabatar da fim da wasan kwaikwayo fiye da 50 masu amfani da harsunan Turanci, da Faransanci, da Larabci, da Portigi, da Kiswahili, da Hausa wadanda CMG ya fassara a kasashen Afirka har na tsawon wata daya. Masu kallo na kasashen Afirka za su kalli al’adun kasar Sin ta wadannan fina-finai da wasan kwaikwayo, kana za su samu damar shiga gasar kacici-kacici da halartar bukukuwan. (Zainab)