logo

HAUSA

Lokacin yin binciken asalin kwayar cutar COVID-19 a kasar Amurka ya yi

2021-11-01 16:02:16 CRI

Lokacin yin binciken asalin kwayar cutar COVID-19 a kasar Amurka ya yi_fororder_1101-02

A kwanakin baya, ofishin shugaban kula da harkokin leken asiri na kasar Amurka, ya gabatar da rahoton bincike game da asalin kwayar cutar COVID-19.

An gabatar da rahoton, a daidai lokacin bude taron koli na kungiyar G20 na birnin Rome, kuma abu mafi jawo hankali da aka tattauna a gun taron kolin shi ne yadda ake yaki da cutar COVID-19. Haka zalika kuma, hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, tana shirya aikin neman asalin kwayar cutar COVID-19 a mataki na biyu.

Hukumar leken asiri ta kasar Amurka ta gabatar da rahoton bincike game da asalin kwayar cutar COVID-19 a wannan lokaci, wanda hakan ya shaida cewa, Amurka ba ta bi hanyar daukar alhakin membobin kungiyar G20 ba, kuma tana yunkurin tilastawa hukumar WHO yin aiki a mataki na biyu bisa ra’ayinta.

A kwanakin baya, wakilan kasashe fiye da 80 sun mika wasiku ga babban direktan hukumar WHO, ko bayar da sanarwa ga hukumar, don bayyana goyon bayansu ga Sin da hukumar WHO a hadin gwiwar yin nazari da gabatar da rahoto tare. Kana jam’iyyu da kungiyoyin al’umma da masana fiye da 300, daga kasashe da yankuna fiye da 100, sun gabatar da hadaddiyar sanarwa ga sakatariyar sakataren hukumar WHO, game da kin amincewa da siyasantar da aikin binciken asalin kwayar cutar COVID-19. A gun taron kolin na kungiyar G20 na birnin Rome da aka gudanar, Sin ta jaddada cewa, hadin gwiwa shi ne makami mafi karfi, kana kiran hadin gwiwar samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 da Sin ta gabatar ya samu goyon baya daga kasa da kasa, kuma babu shakka wannan ne abin da ake bukata wajen yaki da cutar COVID-19 a duniya.

Sin ta ce tilas ne Amurka ta dakatar da yin yunkurin siyasa, da nuna goyon baya ga aikin binciken asalin kwayar cutar COVID-19. Kana ya kamata Amurka ta amsa kiran kasa da kasa, da bude dakin gwaji na Fort Detrick, da asusun gwajin binciken halittu, don karbar binciken da masanan hukumar WHO za su iya gudanar. (Zainab)