logo

HAUSA

Tsohon mataimakin wakilin Najeriya a MDD: Kasar Sin na bada babbar gudummawa wajen bunkasa ci gaban duniya

2021-11-02 14:52:42 CRI

Tsohon mataimakin wakilin Najeriya a MDD: Kasar Sin na bada babbar gudummawa wajen bunkasa ci gaban duniya_fororder_微信图片_20211031163021

Bana ake cika shekaru 50 da Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ta maido da halastaccen wakilcinta a Majalisar Dinkin Duniya. Game da wannan batu, Murtala Zhang ya zanta da Ambasada Usman Sarki, wanda shi ne tsohon mataimakin wakilin dindindin na Najeriya da yayi aiki a Majalisar Dinkin Duniya tsakanin shekara ta 2012 zuwa ta 2016.

Ambasada Usman Sarki ya bayyana ra’ayinsa kan muhimmiyar rawar da kasar Sin ta taka a duk fadin duniya baki daya, musamman a fannonin da suka shafi tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, yaki da annobar COVID-19, da kuma tallata ra’ayin halartar bangarori daban-daban a harkokin kasa da kasa. (Murtala Zhang)