logo

HAUSA

Kasashen duniya na taron COP26 don tinkarar matsalolin sauyin yanayi

2021-11-01 11:26:27 CRI

Kasashen duniya na taron COP26 don tinkarar matsalolin sauyin yanayi_fororder_211101-COP26.A3

A jiya Lahadi aka bude taron kolin MDD kan sauyin yanayi (COP26), karo na 26, a birnin Glasgow na kasar Scotland, wanda aka jinkirta gudanarwa da tsawon shekara guda sakamakon annobar COVID-19.

Taron kolin na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar karuwar matsalolin sauyin yanayi dake shafar bala’un dumamar yanayi da matsanancin ambaliyar ruwa da gobarar daji.

Manyan ajandojin da taron kolin zai mayar da hankali sun hada da batun kammala yarjejeniyar Paris game da cika alkawurran samar da kudade daga kasashe masu arziki zuwa kasashe masu tasowa domin taimaka musu wajen tinkarar matsalolin dake shafar sauyin yanayi. (Ahmad)