logo

HAUSA

Jam’iyya mai mulkin Zimbabwe ta lamincewa Mnangagwa ya yi takarar shugabancin kasa a zaben 2023

2021-11-01 10:50:10 CRI

Jam’iyya mai mulkin Zimbabwe ta lamincewa Mnangagwa ya yi takarar shugabancin kasa a zaben 2023_fororder_211101-Zimbabwe.A1

ZANU-PF, jam’iyya mai mulkin kasar Zimbabwe ta sahhalewa shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa, a matsayin dan takarar shugabancin kasar a zaben shekarar 2023.

Amincewar ya zo ne a lokacin babban taron jam’iyyar na shekara wanda aka kammala a ranar Asabar a garin Bindura, mai tazarar kilomita 60 dake arewacin birnin Harare.

A cewar jaridar Sunday Mail, mallakin gwamnatin kasar, mai rikon kakakin jam’iyyar, Mike Bimha, ya ce matakin amincewa da takarar Mnangagwa ya samu gagarumin goyon baya ba tare da hamayya ba.

Bimha ya ce, taron ya zartas da kudurin motsa jam’iyyar domin shirye shiryen tinkarar zaben shekarar 2023.

Haka zalika taron ya kuma sanar da daukar matakin ladaftarwa kan mambobin jam’iyyar da suka nuna rashin da’a wadanda aka samu da laifukan tayar da rikici da sauran laifukan dake shafar rashawa da amfani da mukamansu wajen aikata rashin gaskiya. (Ahmad)