logo

HAUSA

Sin tana goyon bayan jama’ar Zimbabwe tare da adawa da tsoma baki daga waje

2021-11-01 21:48:16 CRI

Sin tana goyon bayan jama’ar Zimbabwe tare da adawa da tsoma baki daga waje_fororder_rBABC2F82CGAcMXIAAAAAAAAAAA493.1024x697.800x545

Dangane da shawarar da wakilin musamman na MDD ya bayar cewa, kasashen da abin ya shafa da su gaggauta janye takunkumin bai daya da suka kakaba wa kasar Zimbabwe, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka yi Litinin din cewa, kasar Sin na adawa da duk wani takunkumi na bai daya, kana tana goyon bayan jama'ar kasar Zimbabwe tare da nuna adawa da tsoma baki daga waje, da daukar hanyar ci gaba mai zaman kanta.

Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar 28 ga wata, wakilin musamman na MDD kan yadda takunkuman bai daya suke haifar da illoli ga yancin bil Adama, a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, ya ba da shawarar cewa, kasashen Amurka, da Birtaniya da sauran kasashen yammacin duniya, sun kakaba wa Zimbabwe takunkumi na bai daya, inda hakan ya yi mummunar illa ga tattalin arzikin Zimbabwe tare da take hakkin bil Adama na jama'ar kasar ta Zimbabwe, ciki har da 'yancin rayuwa, da na abinci, lafiya,da ci gaba, ilimi, da 'yancin tattalin arziki da al'adu. A don haka, ya kamata kasashen da abin ya shafa su dage takunkumin da suka kakaba wa Zimbabwe ba tare da bata lokaci ba.