logo

HAUSA

Jam’iyyun siyasa a Afirka ta kudu sun kammala yakin neman zabe

2021-11-01 11:04:32 CRI

Jam’iyyun siyasa a Afirka ta kudu sun kammala yakin neman zabe_fororder_21101-SA-S2

Jam’iyyun siyasa a Afirka ta kudu, sun kammala yakin neman zabe a karshen mako, gabanin zaben kananan hukumomin kasar da za a kada a Litinin din nan.

Wakilan jam’iyyun kasar sun karkare yakin neman zabe a birnin Cape Town, a gabar da adadin al’ummun kasar kimanin miliyan 1.1 da suka yi rajistar zabe na musamman, suka fara kada nasu kuri’un tun a karshen mako.

Da yake tsokaci yayin yakin neman zaben, shugaban kasar Cyril Ramaphosa, wanda kuma shi ne jagoran jam’iyyar ANC mai mulkin kasar, ya ce ANC za ta iya yin kokarinta, wajen lashe zaben biranen dake lardin yammacin Cape, ciki har da Cape Town. Ya kuma bayyana cewa, ANC za ta kawo managarcin sauyi, duba da yadda take sake salo, da kara gina kanta, domin sauke nauyin dake wuyanta, da warware matsalolin al’umma.

A nasa tsokaci kuwa, sakataren jam’iyyar GOOD, kuma dan takarar neman kujerar magajin garin Cape Town karkashin jam’iyyar, Mr. Brett Herron, cewa ya yi jam’iyyun kasar sun fafata matuka a yakin neman zabe na bana. Ya ce duk da kalubalen annobar COVID-19 da ake fuskanta, wanda ya tilasta takaita al’amura, yakin neman zaben ya yi armashi. Mr. Herron ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, gabanin yakin neman zabensa a garin Mitchells Plain. (Saminu)