Yadda Gao Jie yake kokarin bunkasawa wasan Wushu a kasar Sin da duniya baki daya
2021-11-01 09:11:31 CRI
Wasan Wushu ko kuma wasan Kungfu, wasan gargajiya ne na kasar Sin, wanda yake da tarihin tsawon shekaru 4200. Al’ummar duniya na ganin cewa, wasan Wushu wata alamar musamman ce ta kasar Sin. Wasan Wushu yana kunshe da fasahohi iri daban daban, kamar wasan karate na Tai Chi, fasahar wasan takobi, fasahar wasan wuka, fasahar sarrafa sanda da sauransu, wadanda suka jawo hankalin jama’ar kasar Sin sosai, har ma da duniya baki daya.
Gao Jie, wani dalibi ne mai koyon wasan Wushu a jami’ar koyon ilmin wasannin motsa jiki ta Shanghai ta kasar Sin.
Gao Jie ya fara koyon fasahohin wasan Wushu tun yana da kimanin shekaru 10 da haihuwa, dalilin da ya sa iyayensa suka sa shi koyon wasan shi ne, lafiyar jikinsa domin ba shi da lafiya sosai a lokacin yana yaro. Da farko dai, Gao Jie yana sha’awar wasan Wushu ne kawai, amma bayan da ya koyi wasan daga baya, ya gano wasan Wushu ya sha bambanta da sauran wasannin motsa jiki. Ya ce, malaman dake koya masa fasahohin wasan Wushu suna da bambanci da sauran malaman dake koyar da wasannin motsa jiki. Gao Jie ya ce,“Akwai wani karin magana na kasar Sin dake cewar, ya kamata a nuna da’a kafin a fara koyon fasahohin wasan Wushu. Kafin malamai suka fara koyar mana fasahohin wasan Wushu, da farko dai sun koya mana yadda mutum zai zama mai kyawawa halaye. An fi maida hankali ga halayen masu koyon wasan Wushu. Idan i mutum ba shi da kyawawan halaye, to malamai ba za su koya masa fasahohin wasan Wushu ba.”
Gao Jie ya kiyaye koyon fasaha a mataki na farko na wasan Wushu har tsawon wasu shekaru, wannan ita ce fasahar farko ta wasan. Ya ce wannan fasaha tana da wuya sosai, ya kamata ya koyi fara lankwasa gabobi, yana jin ciwo sosai har sai da ya yi kuka. A lokacin, malamanmu ba su yarda iyayena su kalli yadda nake samun horon wasan ba, domin za su ji tausayi sa
A ganinsa, wasan Wushu yana shafar fannoni daban daban kan wasannin motsa jiki, kamar inganta fasahar lankwasa jiki, da karfin jiki da sauransu. Don haka, bayan da Gao Jie ya shiga jami’a, ya koyi sauran fasahohin wasannin motsa jiki cikin sauri. Kana wasan Wushu ya kara masa lafiyar jiki, tare da gina kyawawan halayensa na nuna kokari don cimma burinsa da kuma zama mai karfin hali a zaman rayuwarsa.
Gao Jie ya lashe lambobin yabo da dama a gasannin wasan Wushu na kasar Sin iri daban daban, amma bai samu damar halartar gasar wasan a matakin kasashen waje ba. Yana fatan idan ya samu dama, zai gabatar da fasahohin wasan Wushu na gargajiya na kasar Sin ga kasashen duniya.
A sakamakon kwarewar fasaharsa a wasan Wushu, Gao Jie ya samu damar shiga kungiyar wasan dragon ta birnin Shanghai, wato kungiya mafi kwarewa a wannan fanni a kasar Sin. Kungiyarsa tana shirin halartar gasar wasan Wushu ta duniya na bana a wata mai zuwa. A ganinsa, akwai alaka a tsakanin fasahohin wasan Wushu da na wasan dragon, wannan zai ba shi sauki shiga horon wasan dragon, idan yana kwarewa kan wasan Wushu.
Gao Jie ya ce, an kafa kwalejin koyon ilmin wasan Wushu a cikin jami’arsa, saboda yadda kasar Sin ko kuma jami’arsa suna kara maida hankali ga bunkasa wasan Wushu na gargajiya na kasar Sin. Koda yake, shi ba kwararren dan wasan Wushu domin shiga gasannin duniya ba ne, amma shi da abokan karatunsu, suna mayar da hankali kan harkokin karatu don ba da gudummawarsu wajen bunkasa sha’anin wasan Wushu a kasar Sin da ma duniya baki daya.
Abokan karatunsa sun kan yabawa Gao Jie, saboda kokarin da yake wajen raya fasahohinsa na wasan Wushu tare da kare kwarewarsa a wasan. Kokarin da yayi ya kan burge abokan karatunsa sosai. Huang Haijing, daya daga cikin abokan karatunsa kuma abokinsa da suke zaune a daki guda da Gao Jie, ya bayyana cewa, sha’awar da Gao Jie ya nuna a wasan Wushu da kokarinsa na raya fasahohi da ilminsa kan wasan, sun burge shi sosai. Kana a ganinsa, wasan Wushu ya yi babban tasiri ga zaman rayuwar Gao Jie. Ya ce,“Gao Jie shi da kansa yana sha’awar wasan Wushu kwarai, kana wasan Wushu ya karfafa zuciyar Gao Jie tare da kiyaye kyawawan halaye a zaman rayuwasa.”
Yayin da yake kokarin koyon ilmi da fasaha a jami’a, Gao Jie ya gano cewa, ana iya hada wasan Wushu da sauran fannoni don raya su baki daya. Gao Jie ya ce,“A ganina, ba ma kawai wasan Wushu yana iya hada kan sauran wasannin motsa jiki ba, hatta ma yana iya hada kan fannin likitanci da kuma na samar da ilmi. Alal misali, a yayin da ake kokarin yaki da cutar COVID-19, al’ummar kasar Sin da dama suna kokarin koyon da ma yin wani irin wasan Wushu mai suna Baduanjin.”
Game da bunkasuwar wasan Wushu, Gao Jie ya ce, yanzu wasan Wushu yana samun karbuwa sosai a kasar Sin, kana idan dan wasan Wushu yana son inganta fasahohinsa na wasan Wushu sosai, dole ne ya zabi samun horo a kasar Sin. Gao Jie ya ce,“Wasan Wushu wasa ne na gargajiya na al’ummar kasar Sin, wanda ya samu ci gaba sosai a cikin kasar Sin, kana akwai ‘yan wasan da dama da ya shahara a duniya da suka kware a kasar Sin. Idan ‘yan wasa daga kasashen waje suna son samun ci gaba a fannin wasan Wushu, ana bukatar su rika samun horo a kasar Sin.”
LIN WEI WAFA RODOLPHO, abokan karatun Gao Jie ne daga kasar Benin, ya ce yana sha’awar wasan Wushu tun yana kuriciyarsa, kana yana samun kwarewa sosai kan wasannin motsa jiki a kasarsa, amma saida ya samu damar zuwa kasar Sin don koyon ilmin wasannin motsa jiki a kasar Sin. Lokacin da ya zo kasar Sin ya kuma shiga jami’a, ya zabi koyon ilmin wasan Wushu kai tsaye. Ya ce,“Ina fatan wasan Wushu zai shiga gasar wasannin Olympics, kana na samu karin dama wajen yada wasan Wushu a kasarmu.”
Kana Gao Jie yana kokarin ci gaba da bunkasa wasan Wushu a cikin kasar Sin, kamar yada wasan a cikin makarantun firamare da midil, ya ce, a sakamakon samun ci gaban wasan a kasar Sin, makarantu da dama sun bude ajin musamman na koyar da wasan Wushu ga dalibansu. Ban da wannan kuma, Gao Jie yana koyar da wasu ‘yan wasan Wushu dabarun wasan, tare da yin nazari kan yadda ake samun horon da ya dace
A karshe dai, Gao Jie ya yi kira da a nuna kulawa mai kyau ga dukkan ‘yan wasa, domin babu wanda ya san irin kokarin da ‘yan wasa suka yi, da tsawon lokaci na samun horo, don haka bai kamata a rka yi musu kalaman da ba su dace ba, idan ‘yan wasa ba su samu kyakkyawan sakamako a gasanninsu ba, yana fatan dukkan jama’a za su nuna musu kauna, da ba su goyon baya, a hakika suna shan wahala sosai.
A matsayinsa na mai nazarin ilmin wasannin motsa jiki, Gao Jie yana son yin amfani da kimiyya da ilmin da ya samu, don kara samar hanyoyin samun horo mafi dacewa ga ‘yan wasa ta yadda za su samu ci gaban fasahohi a wasansu baki daya. (Zainab Zhang)