logo

HAUSA

COP26: Yadda kasar Sin ke burin ganin an dakile kalubalolin duniya

2021-11-01 16:29:32 CRI

COP26: Yadda kasar Sin ke burin ganin an dakile kalubalolin duniya_fororder_111

A yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar manyan kalubaloli wadanda ke barazana ga rayuwar bil adama har ma da muhallin halittu, sakamakon dalilai na halayyar dan adam gami da wadanda ke faruwa daga indallahi. A karshen wannan mako ne aka bude taron kolin MDD game da tinkarar matsalolin sauyin yanayi karo na 26 wato COP26, a birnin Glasgow, na kasar Scotland. Ko da yake, an samu jinkiri wajen shirya taron har tsawon shekara guda sakamakon barkewar annobar COVID-19. Taron kolin na wannan karo na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke kara fuskantar tarin matsalolin sauyin yanayi dake shafar rayuwar bil adama da muhallin halittu, kama daga matsalar dumamar yanayi wadda ke haddasa matsanancin fari da yaduwar cutuka, ga kuma matsalolin mummunar ambaliyar ruwa da gobarar daji da makamantansu.

A daidai lokacin da duniyar ke fuskantar wadannan kalubaloli, za mu iya cewa, tamkar abin da masu hikimar magana ke fadi ne cewa, “kaya ya tsinke a gindin kaba”. Domin kuwa a karshen wannan mako ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada gwiwa da juna domin tinkarar manyan kalubalolin duniya, shugaban ya ce, nasarar hakan ya dogara ne kan daukan kwararan matakai na bai daya. Hakika, duniya tana bukatar hadin gwiwar dukkan bangarori domin hada karfi da karfe don cire kitse daga wuta. Yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a wajen taron shugabannin kasashen G20 karo na 16 ta kafar bidiyo a makon da ya gabata, shugaba Xi ya yi tsokaci cewa, a shekarun baya bayan nan, ana yawan samun karuwar mummunan sauyin yanayi kuma akwai bukatar gaggawa ta daidaita karuwar sauyin yanayin.

A cewar shugaban, kwan-gaba kwan-bayan da ake samu ta fannin kasuwar makamashi ta kasa da kasa ya kara tunatar da mu cewa tilas ne mu yi kokarin aiwatar da aikin kare muhalli a yayin da muke raya tattalin arziki, kana mu dauki matakan magance matsalolin sauyin yanayi da kare rayuwar al’umma. Xi Jinping ya bayyana cewa, magance matsalolin sauyin yanayi da gyara tsarin samar da makamashi sun dogara ne kan ci gaban fasaha. Ya kamata mambobin G20 su jagoranci ayyukan bunkasuwa da kuma amfani da fasahohin zamani. Kamata ya yi kasashen da suka ci gaba su cika alkawuran da suka dauka kana su samar da kudaden tallafawa kasashe masu tasowa. (Ahmad Fagam)