logo

HAUSA

Sin ta ba da shawarwari 5 don ingiza sauke nauyin dake wuyan G20

2021-10-31 16:39:17 CRI

Sin ta ba da shawarwari 5 don ingiza sauke nauyin dake wuyan G20_fororder_微信图片_20211031163854

Jiya Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shugabannin G20 karo na 16 a mataki na farko ta kafar bidiyo, inda cikin jawabinsa ya gabatar da wasu shawarwari 5 a matsayin hanyoyin mafi dacewa wajen sauke nauyin dake wuyan kasashen G20, matakin da ya bayyana nauyinta na wata babbar kasa.

Wadannan shawarwari sun hada da batun hadin kai don tinkarar COVID-19; kara yin cudanya da juna don ingiza farfadowar tattalin arziki; yin hakuri da juna da samun bunkasuwa tare; fitar da sabbin hanyoyi ta hanyar kirkire-kirkire; samun bunkasuwa tare da kiyaye muhalli, wadannan shawarwarin sun dace da abubuwan da suke janyo hankalin kasashen duniya, abin da ya fitar da wata hanya ta samun bunkasuwa tare.

A cikin jawabinsa shugaba Xi Jinping ya ce, aiwatar da manufar gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da ingiza kafa kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya, abu ne da ya dace da jigon taron na wawnnan karo wato “Dan Adam da duniya da samun wadata”, haka  kuma ya bayyana nauyin dake bisa wuyan kasashen G20 na jagorantar kwaskwarimar da kasashen duniya za su yi kan tattalin arziki. A matsayinta na muhimmiyar mamba kana kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, Sin za ta ci gaba da bude kofarta da samar da sabon zarafi bisa ci gaban da take samu don ba da gudunmawa mai karfi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya da sa kaimi ga kasashen G20 da su sauke nauyin dake bisa wuyansu. (Amina Xu)