logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da babban daraktan hukumar WHO Tedros Ghebreyesus

2021-10-31 17:19:55 CRI

Wang Yi ya gana da babban daraktan hukumar WHO Tedros Ghebreyesus_fororder_W020211031356874287075

Jiya Asabar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Ghebreyesus a birnin Rome na kasar Italiya.

A ganawar tasu, Wang Yi ya nuna cewa, a cikin shekara daya da wani abu da suka gabata, jama’ar kasar Sin sun samu ci gaba mai armashi wajen yaki da cutar COVID-19 karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping. Ba ma kawai Sin ta yi kokarin tinkarar cutar a kasar ba, har ma ta baiwa sauran kasashe tallafin jin kai cikin gaggawa bisa tunanin makomar Bil Adama ta bai daya a fannin kiwon lafiya. Hukumar WHO ce jigon yaki da cutar a duniya, Sin na dora muhimmanci matuka kan gudunmawar da hukumar ke bayarwa ga duniya, Sin na kara hada kanta da kasashen duniya ta fuskar rarraba allurar rigakafi cikin daidaito da fitar da sabbin magunguna da kara marawa kasashen Afrika goyon baya a fannin yaki da cutar, ta yadda za ta taka rawarta a wannan fanni a duniya.

A nasa tsokaci, Tedros Ghebreyesus ya nuna cewa, cutar abokiyar gabar dukkanin kasashen duniya ce. Hukumarsa tana jinjinawa ra’ayin hadin kai da Sin take dauka, yana kuma goyon bayan taimakon da Sin take baiwa kasashe daban-daban wajen yakar cutar, da yabawa gudunmawar da Sin take bayarwa wajen rarraba alluran cikin daidaito da shigarta shirin COVAX. WHO tana nacewa kan matsayinta, wato ba zata yi kasa a gwiwa ba kan matsin lambar siyasa da ake mata, tana matukar yaki da matakin dora laifi kan wasu, kuma a cewarsa, hukumar za ta nace ga hana siyasantar da batun yaki da cutar, za ta kuma ci gaba da binciken asalin cutar bisa kimiyya da fasaha. (Amina Xu)