logo

HAUSA

Najeriya za ta yi bincike kan matsalolin da ke cikin gidajen yarin kasar

2021-10-31 17:22:08 CRI

Najeriya za ta yi bincike kan matsalolin da ke cikin gidajen yarin kasar_fororder_微信图片_20211031172124

Gwamnatin Najeriya ta sanar cewa, ta kaddamar da kwamitin bincike domin tantance matsalolin da ke cikin gidajen yarin kasar, bayan hare haren da aka kaddamar kan gidajen yari a sassan kasar.

A wata sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Asabar, ministan cikin gida na kasar, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa, a ranar Juma’a an kafa kwamitin bincike domin tantance matsalolin da ke akwai a gidajen gyaran hali dake sassan kasar da irin nakassun da suka haifarwa fannin tsaro.

A cewar hukumomi, ranar 22 ga watan Oktoba, sama da fursunoni 800 ne suka tsere bayan wani harin da ‘yan bindiga suka kaddamar a gidan gyaran hali dake jahar Oyo a shiyyar kudu maso yammacin kasar.(Ahmad)