logo

HAUSA

Babban sakataren EAC: Ana fatan karfafa mu’amala da kasar Sin

2021-10-30 16:35:07 CRI

Babban sakataren EAC: Ana fatan karfafa mu’amala da kasar Sin_fororder_hoto

A ranar 28 ga wata, babban sakataren kungiyar hadin gwiwar gabashin kasashen Afirka wato EAC, Peter Mutuku Mathuki ya bayyana cewa, kungiyar EAC tana fatan koyon fasahohin kasar Sin a fannin neman ci gaba, da kuma karfafa hadin gwiwarta da kasar Sin kan ayyukan yaki da annobar COVID-19, da gina ababen more rayuwa, da kuma raya matasa da dai sauransu.

A wannan rana, sabon jakadan kasar Sin a kasar Tanzaniya, kana jadakan kasar Sin dake kungiyar EAC, Chen Mingjian ya gabatar da takardar kama aiki ga Mista Peter Mutuku Mathuki, a birnin Arusha dake arewacin kasar Tanzaniya. (Maryam)