logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci a dauki matakan daidaita rikicin siyasar Mali

2021-10-30 16:39:04 CMG

Jakadan Sin ya bukaci a dauki matakan daidaita rikicin siyasar Mali_fororder_1030-mali-Ahmad

Wakilin kasar Sin ya bukaci a dauki matakai a matakin cikin gida da kuma na kasa da kasa don tabbatar da warware dambarwar siyasar kasar Mali.

Kasar Mali, ta shafe tsawon lokaci tana fuskantar kalubaloli masu yawan gaske.

Zhang Jun, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, ya bayyana cewa, muddin ana fatan warware matsalolin dake addabar kasar, akwai bukatar yin kokari daga dukkan bangarorin kasar Mali da kuma taimakon kasa da kasa. Babban abinda yafi damun kasar a halin yanzu shine a yi kokarin warware rikicin siyasar Mali da kuma samar da yanayin da al’ummar kasar ta Mali zasu iya jure kalubalolin dake damun kasarsu.

Zhang, ya bayyanawa kwamitin sulhun MDD cewa, kasar Sin tana taimakawa gwamnatin Mali wajen cimma nasarar shirin kafa shugabancin siyasa, da farfado da bin dokokin tsarin mulkin kasa bisa hanya mafi dacewa, haka kuma tana maraba da dukkan matakan da Mali zata dauka wajen karfafa hadin kan kasa ta hanyar tattaunawa da kuma kafa gwamnatin da zata kunshi dukkan bangarorin kasar. A hannu guda kuma, jakadan ya bayyana cewa, tilas ne jadawalin kafa shugabancin kasar Mali ya dace da hakikanin yanayin kasar.

Yace kasar Sin tana goyon bayan kokarin cigaba da tattaunawar da kungiyar tarayyar Afrika AU da kuma ECOWAS ke jagoranta, kana ya karfafa gwiwar kungiyoyin shiyyar dasu zurfafa tuntubar hukumomin kasar Mali domin gina ingantacciyar fahimtar juna.(Ahmad)

Ahmad