logo

HAUSA

Me ya sa ake ta fama da barkewar rikici a kasar Sudan?

2021-10-30 13:38:33 CRI

Me ya sa ake ta fama da barkewar rikici a kasar Sudan?_fororder_rBABCWF3MF-AM8G4AAAAAAAAAAA270.869x505.750x436

Rikici ya sake barkewa a kasar Sudan.

A ranar 25 ga wata, bayan da sassa biyu da ke nuna goyon baya ga soja da ma gwamnatin farar hula suka shafe kwanaki suna zanga zanga a birnin Khartoum, rundunar sojan kasar ta tsare firaministan gwamnatin rikon kwarya na kasar Abdallah Hamdok, a yayin da shugaban majalisar mulkin sojoji na kasar Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan ya sanar da rusa gwamnatin rikon kwaryar kasar, tare da ayyana dokar ta baci a duk fadin kasar.

Me ya sa ake ta fama da barkewar rikici a kasar Sudan?_fororder_rBABCmF3MF-AEkPJAAAAAAAAAAA089.739x415

Rikicin ya auku ne ba zato, sai dai al’ummar kasar ta Sudan sun nuna tamkar sun saba. Sabo da idan ba a manta ba, yau shekaru biyu da rabi da suka gabata, zanga-zangar da aka shafe wasu kwanaki ana yi ta haifar da juyin mulki a kasar, inda aka kama tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir, kuma gwamnatin kasar ta wargaje. Ga shi shekaru biyu da rabi sun wuce, amma kokarin da aka yi na kiyaye dimokuradiyya a kasar tamkar ya bi ruwa.

Me ya sa rikice-rikice suka yi ta barkewa a kasar ta Sudan?

Matsalar rayuwar al’umma a sanadin tabarbarewar tattalin arziki ta kasance babbar matsalar da ke haifar da rikicin siyasa a kasar. A shekarar 2019, yadda aka yi fama da karancin kayayyakin masarufi da suka hada da abinci, da makamashi, ya sa al’umma sun fita tituna, wanda daga karshe ya kifar da mulkin Al-Bashir. Sai dai har yanzu, ba a kai ga warware matsalar ba. Akasarin al’ummar kasar da suka tattauna da ‘yan jarida sun bayyana cewa, bayan juyin mulki a shekarar 2019, “rayuwarmu ba ta kai ta baya ba”.  Wasu kuma sun ce, akwai kudin da ake samarwa ga masu zanga-zanga, wato ana biyan dan kudi ga masu zanga-zanga”, “ba mu da abin yi, a kalla za mu iya samun dan kudin abinci idan mun shiga zanga-zanga”.

Me ya sa ake ta fama da barkewar rikici a kasar Sudan?_fororder_rBABCmF3MGCAMjqqAAAAAAAAAAA738.847x483.750x428

Dangane da mummunan yanayin tattalin arziki da ma mawuyacin halin rayuwar al’umma, ma iya cewa, Amurka da ma sauran kasashen yammacin duniya sun ba da “taimako”. Takunkumin da kasashen suka kakaba wa kasar cikin kusan shekaru 30 da suka wuce, ya yi wa ci gaban tattalin arzikin kasar tarnaki, wanda kuma ya haifar da illa ga rayuwar al’ummar kasar. A daya hannun kuma a shekarar 2011, Sudan ta kudu ta samu ‘yancin kanta bisa kokarin da Amurka ta yi, matakin da ya raba yawancin arzikin man fetur daga kasar. Don haka kuma, gwamnatin kasar ta rasa babban abun da ta dogara da shi wajen samun kudin shiga.

Tattalin arziki da rayuwar al’umma su ne tushen kwanciyar hankalin siyasa. A sakamakon matsalolin da ake fuskanta ta fannonin tattalin arziki da zaman al’umma, aka yi ta fama da tashin hankali a kasar. Baya ga haka, yadda Amurka da ma sauran kasashen yamma suka fake da sunan “kare hakkin dan Adam da dimokuradiyya” wajen tsoma baki cikin harkokin gida na kasar ta Sudan, shi ne ainihin dalilin da ya haifar da tashin hankalin. Misali Amurka ta sha amfani da batun Darfur wajen tsoma baki cikin harkokin hakkin bil Adam da dimokuradiyya na kasar.

Me ya sa ake ta fama da barkewar rikici a kasar Sudan?_fororder_rBABDGF3MGCAO_JXAAAAAAAAAAA998.496x610

Ba ma Sudan kawai ba, mawuyacin hali da kasashe da yawa suke ciki ba ya rasa nasaba da “taimako” da kasashen yamma suka samar.

A kasar Zimbabwe, sakamakon gyare-gyaren da aka yi ta fannin mallakar gonaki, an mika gonaki da a baya ke hannun masu gandun noma fararen fata ga bakaken fata, matakin da ya sa Amurka da Burtaniya da ma sauran kasashen yamma suka kakaba wa kasar takunkumi na tsawon shekaru sama da 20. Ranar 25 ga wata, ta kuma kasance ranar nuna kyamar takunkumin da kungiyar SADC ke gudanarwa. A wannan rana, al’ummar kasar ta Zimbabwe sun gudanar da zanga-zanga a birnin Harare, don nuna adawa da takunkumin da kasashen yamma suka sanya wa kasarsu.

Me ya sa ake ta fama da barkewar rikici a kasar Sudan?_fororder_1127995312_16352086950971n

Akwai kuma Masar, da Libya, da Afghanistan da Myanmar, dukkansu kasashe ne da suka sha illa daga abun da Amurka, da ma sauran kasashen yamma suka kira wai “dimokuradiyya”.  Zaman lafiya da ci gaba ya kasance jigon zamanin da muke ciki. Kowace kasa na da ‘yancin kiyaye zaman lafiya da ci gaba, ‘yancin da ya kamata sauran kasashen duniya su martaba. Dokokin da su Amurka suka tsara ba wai dokoki na kasa da kasa ba.

Ana iya shigar da dimokuradiyya, kasashen da suke yi na’am da tsarin dimokuradiyya na kasashen yamma, to, sai su koya, amma ba za a iya fitar da dimokuradiyya ga sauran kasashe ba, balle a ce a tilastawa wata kasa ta bi tsarin dimokuradiyya na wata. Ba kasa daya kawai a duniya ba, haka kuma ba wai tsari iri guda a duniya ba. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, “Dimokuradiyya ba ‘yancin musamman ne na wata kasa ba, ‘yanci ne na bai daya ga al’ummar kasa da kasa”, “Akwai hanyoyi daban daban wajen kiyaye dimokuradiyya” “Ya kamata a bar al’ummar kasashen duniya su yanke hukunci a game da ko akwai dimokuradiyya a kasar su ko a’a” “Babu tsarin siyasa da ya cancanci yanayin dukkanin kasashe”.

Rashin tsoma baki cikin harkokin gida na sauran kasashe, ya kasance daya daga cikin muhimman ka’idojin cudanyar kasa da kasa, haka kuma manufa ce da kasar Sin ke bi a kullum. Ya kamata a bari al’umma su kula da siyasar kasarsu. Wadanda ke mai da hankali a kan kifar da mulkin sauran kasashe, lallai za su girbi zambar da suka shuka. (Lubabatu)