logo

HAUSA

Amurkawa suna sa ran za a yi nasarar shirya wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing

2021-10-30 16:21:15 CRI

Amurka daya ce daga cikin kasashe wadanda suka fi rinjaye kan wasan kankara, kan batun wasannin Olympics na lokacin hunturun da za a gudanar a birnin Beijing, yawancin al’ummun Amurkawa wadanda suka zanta da manema labarai sun bayyana cewa, suna sa ran za a yi nasarar kaddamar da wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, kuma suna fatan za a kammala shi cikin nasara, haka kuma sun amince cewa, taron wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing zai sake kawo al’ajabi ga duniya.

Wasu sun bayyana cewa, taron wasannin Olympics dandalin gasa ne da aka shirya don ‘yan wasa, ya kamata a mai da hankali kan batun wasannin, bai dace a siyasantar da wasannin ba.(Jamila)