logo

HAUSA

Kwamitin Sulhu na MDD ya bukaci a maido da gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin farar hula a Sudan

2021-10-29 10:56:02 CRI

Kwamitin Sulhu na MDD ya bukaci a maido da gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin farar hula a Sudan_fororder_I03-UN Security Council demands restoration of civilian

MDD ta bukaci a sako shugabannin farar hula da ake tsare da su tare da maido da gwamnatin rikon kwarya da farar hula ke jagoranta a kasar Sudan.

A cikin wata sanarwa da suka fitar, mambobin kwamitin sulhun majalisar, sun bayyana matukar damuwarsu game da kwace mulki da sojoji suka yi a Sudan a ranar Litinin, tare da dakatar da wasu hukumomin rikon kwarya, da kafa dokar ta baci, da tsare firaminista Abdalla Hamdok da wasu fararen hula na gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Mambobin majalisar sun yi kira da a gaggauta sakin dukkan wadanda hukumomin soji ke tsare da su, dangane da haka kuma, sun yi la’akari da komawar firaminista Hamdok gidansa.

Sun kuma bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na kasar, da su shiga tattaunawa ba tare da gindaya wani sharadi ba, domin ba da damar aiwatar da kundin tsarin mulkin kasar, da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a Juba, wadda ta tabbatar da mika mulki ga tsarin dimokiradiyyar Sudan.

Babban kwamandan sojojin Sudan Al-Burhan, ya kori jakadun Sudan a ofishin MDD dake Geneva, da kungiyar Tarayyar Turai, da kasashen Amurka, Faransa, da Sin, da Qatar, saboda nuna goyon bayansu ga firaministan gwamnatin rikon kwarya na Sudan, Abdalla Hamdok, kamar yadda kafofin yada labaran Sudan su ka ruwaito a jiya. (Ibrahim Yaya)