logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kama mutane 9 da ake zargi tare da lalata haramtattun matatun mai guda 27

2021-10-29 10:37:49 CRI

Sojojin Najeriya sun kama mutane 9 da ake zargi tare da lalata haramtattun matatun mai guda 27_fororder_i02-Nigerian troops arrest 9 suspects

Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Bernard Onyeuko, ya bayyana cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kama wasu mutane 9 da ake zargi tare da lalata jimillar wuraren tace man fetur 27 ba bisa ka’ida ba a cikin makwanni biyun da suka gabata.

Kakakin rundunar, ya shaidawa manema labarai a wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, an kuma gano wasu kayayyaki da dama yayin matakan da sojojin suka dauka tsakanin ranar 14 zuwa 28 ga watan Oktoba a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur.

Ya kara da cewa,, sojojin sun kuma yi nasarar kama wasu mutane biyar dake da alaka da fasa bututun mai, da fashin teku, da hada-hadar man fetur ba bisa ka’ida ba, da kuma fashi da makami a cikin wannan lokacin

Bernard Onyeuko ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na wayar tarho cewa, kimanin mako guda da ya gabata ne, wasu mutane da ba a san adadinsu ba suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, sakamakon fashewar wani abu da kuma wata gobara da ta tashi a wata haramtacciyar matatar mai da ke yankin Rumuekpe a jihar Ribas da ke kudancin kasar, wanda shi ma ke yanki mai arzikin man fetur a kasar. (Ibrahim)