logo

HAUSA

Xi Jinping ya zanta da firaministan Birtaniya ta wayar tarho

2021-10-29 20:03:38 CRI

A yau Juma’a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da firaministan Birtaniya Boris Johnson ta wayar tarho. Yayin zantawar ta su, shugaba Xi ya ce Sin da Birtaniya, kasashe ne dake da kujerun dindindin a kwamitin tsaron MDD, kuma suna cikin manyan kasashen duniya masu wadata.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, ya kamata sassan biyu su kara kyautata tattaunawa, da karfafa hadin gwiwar ba da gudummawa ga nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a matakin kasa da kasa, da kyautata jagorancin duniya, da ingiza ci gaba da zaman lumana.

A nasa bangaren kuwa, Mr. Johnson cewa ya yi, Birtaniya da Sin na cimma matsaya daya, suna kuma da moriya ta bai daya a muhimman batutuwa da dama, kamar fannin kiwon lafiya, da na farfadowar tattalin arzikin duniya.  (Saminu)