logo

HAUSA

Sin ta yi rawar gani a fannin yayata matakan dakile sauyin yanayi

2021-10-28 20:20:43 CRI

Sin ta yi rawar gani a fannin yayata matakan dakile sauyin yanayi_fororder_yanayi

A shekarun baya bayan nan, a gabar da ake kara azamar aiwatar da matakai daban daban, na yayata muhimmancin dakile sauyin yanayi, aiwatar da matakan shawo kan wannan kalubale sun zama gama duniya tsakanin sassan kasa da kasa.

A baya bayan nan, jami’an kasar Sin sun fitar da takardar bayani mai taken "Manufofin Sin da matakan ta na shawo kan sauyin yanayi”, takardar da ta yi fashin baki ga kasa da kasa game da nasara, da ci gaban da kasar ta cimma a wannan fanni, kana ta yi bayani dalla dalla game da matakan Sin na tabbatar da ta sauke nauyin dake wuyan ta a matakin kasa da kasa, tare da ingiza aikin kafa al’ummar duniya mai makomar bai daya.

Wannan ne karo na 2 tun baya shekarar 2011, da kasar Sin ta fitar da takardar bayani, mai fayyace matakan ta na yaki da sauyin yanayi a matakin kasa.

Daga wannan mataki, abu ne mai sauki a gane cewa, har kullum Sin na kan gaba, wajen yayata matakan dakile sauyi yanayi.  (Saminu)