Tinkarar Sauyin yanayi: Kyan alkawari cikawa
2021-10-28 20:23:23 CMG
Wata takardar bayanin da kasar Sin ta fitar a jiya Laraba ta nuna cewa, kasar Sin tana kokarin cika alkawarin da ta dauka na tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya, don tabbatar da makoma mai haske ga dan Adam.
Batun sauyin yanayi ya shafi kowa, saboda kwararru masu nazarin yanayi suna ganin cewa, idan matsakaicin zafin yanayi na duniya ya karu da digiri 2, hakan zai haddasa bala’u daga Indallahi irinsu hauhawar matsayin teku, da ambaliyar ruwa, da mahaukaciyar guguwa, da kuma fari, wadanda za su kashe dukkan dan Adam.
Yanzu haka a Najeriya, sauyin yanayi na haifar da matsalolin kwararowar hamada, da fari, da lalacewar aikin gona, gami da wasu matsaloli masu alaka da al’umma, irinsu rikicin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma, da matsalar tsaro, da ta’addanci, da dai sauransu.
Idan an dubi hoton bayanai din dake sama, za a iya ganin yadda zafin yanayi ya karu da kimanin digiri 1, cikin shekaru dari daya da suka wuce, bayan da aka fara kaddamar da fasahohin masana’antu a Turai. Yadda kasashe daban daban, musamman ma kasashe masu sukuni, suka dinga yin amfani da makamashin da suka hada da kwal, da mai da dai sauransu don raya masana’antu, ya sa an samun karin iska mai dumama yanayi, wadda ta sa zafin yanayi ke rika karuwa. Wannan shi ne dalilin da ya ake bukatar takaita fitar da iska mai dumama yanayi.
A kasar Sin,gwamnati ta maida rage iskamaidumamayanayi, da samun cigabamaidorewa, a matsayinwatababbarmanufa.Takardarbayanin da kasarSin ta gabatar a wannankaro ta nunacewa, dagashekarar 2015 zuwa ta 2020,yawaniskamaidumamayanayi da aka fitar a kasarSin,ta ragu da kashi 18.8%. Kana adadinyaragu da kashi 48.8%,idanankwatanta da jimilarshekarar 2005.Yanzuwanisabonburin dakasar Sin ta sanyagaba,shi ne sanyayawaniskamaidumamayanayin da kasarkefitarwata kai kolikafinshekarar 2030,watoadadinyadainakaruwa.Sa’annankasar za ta yi kokarin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060.
Ban da wannan kuma, kasar Sin na kokarin taimakawa sauran kasashe masu tasowa, a fannin tinkarar sauyin yanayi. Tun daga shekarar 2011, kasar Sin ta ware dala miliyan 190 don tallafawa hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen masu tasowa a kokarin tinkarar sauyin yanayin duniya. Kana kasar ta kulla kwantiragi 40 tare da kasashe 35, da taimaka musu gina yankunan nuna fasahohin rage fitar da iska mai dumama yanayi, da samar musu da kayayyakin da suke bukata. A watan Satumban bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, kasar Sin za ta taimaki sauran kasashe masu tasowa wajen raya makamashi mai tsabta, kana ba za ta gina tashar samar da wutar lantarki ta hanyar kone kwal a sauran kasashe ba.
Ta wadannan abubuwa za mu iya ganin kokarin da kasar Sin take yi, don kare bil Adama daga mummunar illar da sauyin yanayi zai iya haifar. Sai dai ba za a samu cimma burin ba, da gudunmowar da kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa kadai suke samarwa. Hakika kasashe masu sukuni sun fi samar da iska mai dumama yanayi a tarihin dan Adam, don haka ya kamata su dauki karin nauyi a kokarin daidaita matsalar sauyin yanayi. Amma abun da ya faru shi ne, a wani bangare, su kasashe masu sukuni suna tsumulmula, ba su son samar da kudi, da fasahohi ga kasashe masu tasowa, yayin da a wani bangaren na daban, suna fatan ganin kasashe masu tasowa na daukar karin nauyi. Haka zalika, wasu kasashe masu sukuni su kan yi alkawari, amma ba tare da neman cika su ba. Dangane da wadannan kasashe, kasar Sin ta dade tana kokarin lallashinsu cewa, wato dai dole ne a dauki nagartattun matakai, ta yadda za a iya samun damar tinkarar sauyin yanayi.
Hausawa su kan ce “Kyan alkawari cikawa”. A fannin daidaita matsalar sauyin yanayi, kasar Sin ta yi ta kokarin cika alkawuran da ta yi. Yanzu sai mu duba yadda kasashe masu sukuni za su cika alkawuransu. (Bello Wang)